in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin za ta gina sojojin jiragen ruwa da ke iya aiwatar da ayyukan soja irin daban daban da kyau
2010-03-08 15:31:56 cri

A ran 8 ga wata, a birnin Beijing, wakilin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin kuma mataimakin kwamanda rukunin jiragen ruwan sojojin kasar Sin da ke a tekun gabashin kasar Zhang Huachen ya bayyana cewa, aikin kare jiragen ruwan kasuwanci dake zirga-ziraga a Gulf Aden da Somaliya wannan ya samar da sabbin bukatun ga sojojin jiragen ruwa na kasar Sin a fannonin inganta kayayyakin soja da bunkasuwar sojojin jiragen ruwa da aikin horar da sojojin da sauransu. Kuma kasar Sin za ta gina sojojin jiragen ruwa da ke iya aiwatar da aikin ceto da yaki da 'yan fashin teku da ayyukan soja irin daban daban da kyau.

Zhang Huachen ya bayyana wa manema labaru cewa, ya zuwa yanzu, sojojin jiragen ruwan kasar Sin sun aiwatar da aikin kare jiragen ruwa kasuwanci sau 173, kuma yawan jiragen ruwan kasuwanci da sojojin jiragen ruwan kasar Sin suka kare ya kai 1660, daga cikinsu akwai jiragen ruwan kasashen waje 557, kuma sojojin jiragen ruwan kasar Sin sun aiwatar da aikin ceto jiragen ruwan da aka sace sau 10 ko fiye. Aikin kare jiragen ruwa a tekun Somaliya ya tabbatar da karfin sojojin jiragen ruwan kasar Sin, a sa'i daya kuma, ya tabbatar da cewa kasar Sin tana kokari wajen kiyaye zaman lafiya a duniya da yankuna daban daban.(Abubakar)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China