in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bankin ICBC zai kara bayar da rancen kudi ga sana'o'in rage hayaki
2010-03-08 15:07:39 cri

A ran 7 ga wata, memban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta jama'ar kasar Sin kuma shugaban bankin ICBC da ke halartar taron majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta jama'ar kasar Sin da ake shirya a birnin Beijing Yang Kaisheng ya bayyana wa manema labaru cewa, yawan rancen kudin da bankin ICBC zai samar wa sana'o'in da suka shafi rage hayaki ya kai kimanin kudin Sin yuan biliyan 400, a shekara bana, bankin zai kara ba da rancen kudi ga wadannan sana'o'i.

Kamfanonin masu samu rancen kudi daga bankin ICBC da suka dace da tsarin kiyaye muhalli ya kai kashi 98 cikin dari, kuma rancen kudin da ya dace da tsarin kiyaye muhalli ya kai kashi 99 cikin dari. Yang Kaisheng ya bayyana cewa, bisa bukatar hukumomin kiyaye muhalli, bankin ICBC ya samar wa kamfanonin da ke da alamar kiyaye muhalli rancen kudi, don tabbatar da ganin an yi amfani da wannan rancen kudi a fannin kiyaye muhalli.(Abubakar)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China