in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin na fatan kara amincewa da juna da hadin gwiwa tsakaninta da kasashe daban daban, don tabbatar da samun bunkasuwa tare
2010-03-07 19:42:43 cri

A ranar 7 ga wata, a gun taron manema labaru na taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama'a ta kasar Sin, ministan harkokin waje na kasar Sin Yang Jiechi ya bayyana cewa, a shekarar 2010 kasar Sin za ta ci gaba da inganta yanayin diplomasiya a dukkan fannoni, da yin iyakacin kokari don kara taka muhimmiyar rawa kan samun zaman lafiya da samun tabbaci a duniya da shiyya-shiyya.

A ranar 7 ga wata, an shirya taron manema labaru na taro na uku na majalisar wakilan jama'a ta kasar Sin, inda ministan harkokin waje na kasar, Yang Jiechi ya amsa tambayoyin da manema labaru na gida da na waje suka bayar dangane da muhimman ayyukan diplomasiya na Sin a shekarar da muke ciki, da dangantaka tsakanin kasashen Sin da Amurka, da dangantaka tsakanin kasashen Sin da Rasha, da taron koli na G20, da batun nukiliya na zirin Korea, da kuma sauran batutuwan dake jawo hankalin duniya. Yang Jiechi ya ce, shekarar 2010 muhimmiyar shekara ce ta ci gaba da fuskantar matsalar kudi ta duniya, da inganta samun farfadowar tattalin arzikin duniya. A wannan shekara kuma, kasar Sin za ta ci gaba da yin tsayin daka kan kiyaye mulkin kai, da kwanciyar hankali, da kuma moriyarta wajen samun bunkasuwa. Yang Jiechi ya kara da cewa, 'A shekarar da muke ciki, za mu gudanar da harkokin diplomasiya na taron koli, da na bikin baje koli na kasa da kasa a birnin Shanghai, a sa'i daya kuma, za mu kafa wani yanayi mai kyau don neman samun tabbaci, da inganta samun bunkasuwa, da kuma daidaita tsarin masana'antu.'

An ce, akwai kasashe fiye da 190, da kungiyoyin duniya sama da 50 da suka yi rajista don halartar taron bikin baje koli na kasa da kasa da za a shirya a watan Mayu a birnin Shanghai na kasar Sin. A lokacin, shugabanni kusan dari daya na kasashen ketare, da mahalarta fiye da miliyan daya daga kasashen waje za su halarci ayyukan dake da nasaba da wannan bikin baje koli. Yang Jiechi ya bayyana cewa, wannan ne karo na farko da aka zabi wata kasa mai tasowa don shirya bikin baje koli na kasa da kasa, ba kawai shi ne wani gaggarumin biki a fannonin tattalin arziki, da zamantakewar al'umma, da kimiyya da fasaha, da kuma al'adu ba, har ma ya samar da wata dama mai kyau ga kasar Sin don ta yi koyi da kasashen duniya.
1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China