in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin za ta kara mai da hankali kan kyautata zaman rayuwar jama'a a shekarar 2010
2010-03-06 18:30:27 cri
A sabili da matakan sa kaimi da aka dauka, a shekarar 2009, tattalin arzikin kasar Sin ya karu da kashi 8.7% bisa na makamancin lokaci na shekarar 2008, karuwar da ta fi burin da aka sanya a farkon shekarar bara. Haka zalika kuma, gwamnatin kasar ta samu nasarori da yawa ta fuskar kyautata zaman rayuwar jama'a, abin da ya sa ta samu karbuwa sosai a zukatan jama'ar kasar. Sa'an nan, an ruwaito labari daga wajen taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin da cewa, gwamnatin kasar Sin, yayin da take gyara tattalin arzikin kasar bisa manyan tsare-tsare, za ta kara mai da hankali kan yadda za a kyautata zaman rayuwar jama'a a bana.

A shekarar 2009, kasar Sin ta fara daukan matakan kudi masu yakini da sassauci, inda aka kara zuba jari a kasuwanni, da kara ba da lamuni, don samar da isashen kudi da ci gaban tattalin arziki da al'umma ke bukata, ta yadda aka samu damar tinkarar rikicin hada-hadar kudi da kyau. A wajen taron manema labaru da aka yi a ranar 6 ga wata a wajen taron majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, Zhang Ping, darektan kwamitin raya kasa da yin gyare-gyare na majalisar gudanarwar kasar Sin, ya bayyana cewa, a shekarar bara, kasar Sin ta samu babbar nasara wajen aikin amfana wa jama'a, kamar yadda ya fadi cewa, 'Ta fuskar kyautata zaman rayuwar jama'a, an fi samun nasara a shekarar bara. A fannin samar da guraban ayyukan yi, mun sa mutane fiye da miliyan 11 da suka fara aiki, abin da ya wuce takitin da muka sanya a farkon shekarar bara. Sa'an nan, mun kara kyautata tsarin inshora don tallafawa dattawa da masu fama da cututtuka. Ban da haka kuma, mun inganta tsarin ba da ilimi don neman samar da zaman daidai wa daida a tsakanin al'umma. Haka kuma, mun fitar da shirin yin gyare-gyare kan tsarin aikin kiwon lafiya, don neman warware matsalolin da jama'a kan fuskanta a lokacin da suka fama da rashin lafiya.'

A ranar 5 ga wata, Wen Jiabao, firayin ministan kasar Sin, ya ce, kyautata zaman rayuwar jama'a ya kasance ainihin makasudi ga raya tattalin arzikin kasar Sin, shi ya sa, za a kara mai da hankali kan aikin a shekarar 2010. A ranar 6 ga wata, Xie Xuren, ministan kudin kasar Sin, ya yi alkawarin kara samar da kudi ga aikin inganta zaman rayuwar jama'a, kamar yadda ya bayyana cewa, 'A shekarar bana gwamnatin kasar Sin ta ware kudin Yuan biliyan 992 don tallafawa aikin gina kayan more rayuwa a kauyuka, da goyon bayan aikin gina gidajen zaune masu rahusa, da raya ayyukan ilimi, da kiwon lafiya, da al'adu, da kuma ba da tallafi ga aikin tsimin makamashi da kare muhalli.'

Wani batu mai muhimmanci shi ne, ba a iya kyautata zaman rayuwar jama'a, in ba tare da kara albashin da jama'ar suke samu ba. Kamar yadda Zhang Ping, darektan kwamitin raya kasa da yin gyare-gyare na majalisar gudanarwar kasar Sin, ya ce, 'Da farko dai, za a kara albashin jama'a, musamman ma na wadanda albashinsu bai taka kara ta karya ba. Cikin birane da garuruwa, za a samar da tsarin tabbatar da karuwar albashin 'yan kwadago a kullum kamar yadda ya kamata, da tabbatar da ganin sun samu kudi a lokacin da aka kayyade'.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China