in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin za ta ci gaba da tafiyar da manufa mai yalwa a cewar Xie Xuren
2010-03-06 16:54:35 cri

Ran 6 ga wata da safe, an bude taron manema labaru na taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama'a ta kasar Sin, Mr. Xie Xuren ministan harkokin kudi na kasar Sin ya nuna cewa, a shekarar da muke ciki kasar Sin za ta ci gaba da tafiyar da manufar tattalin arziki mai yalwa, kuma za ta mai da hankali kan "muhimman ayyuka 5".

Wadannan "muhimman ayyuka 5" sun ne, za a kara karfin daidaita tsarin tattalin arziki, da fadada bukatun da ake da su a gida musamman ma bukatun sayayya, da kara ba da tabbaci da kuma kyautata ga zaman rayuwar jama'a, da karfafa yin gyare-gyare kan tsarin haraji, da kyautata aikin kula da harkokin kudi ta hanyar kimiyya da ingancin hanyar yin amfani kasafin kudi tare da sa ido kan alamun hadarin tattalin arziki. [Musa Guo]

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China