Kamfanin dillancin labaru na The Associated Press na kasar Amurka ya ambato Mista Wen Jiabao yana cewa, kasar Sin za ta yi kokarin cimma burinta na samun karuwar yawan kudin kayayyakin da ake samarwa gida da kashi 8% a bana. Haka zalika kuma, rahoton Mista Wen ya bayyana cewa, kasar za ta tabbatar da farfadowar tattalin arzikinta wanda ya zama na 3 a duniya, ta hanyar hana hauhawar farashin kaya da sa ido kan tsarin hada-hadar kudi.
Ban da haka kuma, kamfanin Reuters na kasar Birtaniyya ya ba da labarin cewa, rahoton aikin gwamnatin kasar Sin da Mista Wen Jiabao ya bayar ya sa ana hangen karuwar tattalin arzikin kasar cikin sauri inda ake sa ran ci gaba da samu a nan gaba, sa'an nan, ana kyautata zaton cewa, gwamnatin kasar Sin za ta kara kokari wajen shawo kan hauhawar farashin kaya da aikin ba da lamuni don magance yiwuwar rashin alfanu a fannin tattalin arziki.
A baya ga haka kuma, jaridar Wall Street Journal ta kasar Amurka ta ba da labarin cewa, kasar Sin ta zama mai tattalin arzikin da ya fi saurin bunkasuwa a duniya, sa'an nan, jawabin Mista Wen Jiabao zai bayyana fuskar da tattalin arzikin zai nufa a nan gaba.(Bello Wang)