in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan kasar Sin ya fitar da rahoto kan aikin gwamnati
2010-03-05 17:18:06 cri

Ranar 5 ga wata, a nan birnin Beijing, aka kaddamar da taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin. A yayin taron, firaministan kasar Mista Wen Jiabao ya gabatar da rahoto kan aikin gwamnati ga wakilai kusan dubu 3. A yayin da kasar Sin ke kokarin yaki da rikicin hada-hadar kudi na duniya, da samun farfadowar tattalin arzikinta, wannan rahoto ya nuna hanyar da kasar Sin zata bi bayan da ta fita daga rikicin tattalin arziki da ake fuskanta a duniya. Haka kuma rahoton ya mayar da martani a game da batutuwa da dama, ciki kuwa har da farashin gidaje, da kudin shiga, da aikin jinya da sauran batutuwan da suka jawo hankalin jama'a. Yanzu ga cikakken bayani.

Bisa hakikanin halin da ake ciki a kasar Sin, wannan rahoto ya duba yadda za'a yi yunkurin bunkasa tattalin arziki yadda ya kamata, da yin gyare-gyare kan tsarin tattalin arziki, da kyautata zaman rayuwar jama'a, gami da tabbatar da kwanciyar hankali a matsayin muhimman ayyukan gwamnati a wannan shekara. Rahoton ya nuna kwarin-gwiwa da imani na gwamnatin kasar Sin kan tinkarar kalubale, da daidaita matsalolin da take fuskanta.

A hakika, kasar Sin ta cimma dimbin nasarori a fannin warware matsalar tattalin arziki a shekarar da ta gabata. A shekara ta 2009, gwamnatin kasar ta fitar da shirye-shirye da matakai da dama, dangane da neman bunkasuwa, da daidaita tsari, da sa kaimi ga yin gyare-gyare, gami da kyautata zaman rayuwar jama'a, a kokarin tinkarar matsalar tattalin arziki ta duniya yadda ya kamata. A yayin da ake fama da koma-bayan tattalin arzikin duniya, karuwar tattalin arzikin kasar Sin ya zarce hasashen da aka yi, wanda ya kai kashi 8.7 bisa dari. Haka kuma, karuwar tattalin arzikin kasar Sin na taimakawa sosai wajen farfado da tattalin arzikin duniya baki daya.

Ko da yake ana fuskantar abubuwan rashin sanin tabbas da wahaloli da dama, gwamnatin kasar Sin tana da imani sosai a kokarin raya tattalin arzikinta a wannan shekara. Babban burinta shi ne, yawan GDP zai karu da kashi 8 bisa dari, yawan mutanen da suka yi rajistar rasa rayukansu a birane da garuruwa zai yi kasa da kashi 4.6 bisa dari, haka kuma ma'aunin farashin kayayyakin da mazauna birane ke saya wato CPI zai karu da kashi 3 bisa dari. Game da wadannan burin da aka tsara, Mista Wen Jiabao ya nuna cewa :

"Ina so in jaddada cewa, yayin da ake kokarin cimma burin samun karuwar GDP da kashi 8 bisa dari, ya kamata a mayar da hankali sosai kan kawo sauyi ga hanyar bunkasuwar tattalin arziki, gami da daidaita tsarin tattalin arziki. Haka kuma an yi la'akari da sauran muhimman abubuwa daban-daban, a kokarin tsara burin samun karuwar ma'aunin farashin kayayyakin da mazauna birane ke saya wato CPI."

Domin cimma burin samun karuwar tattalin arziki, a cikin rahoton da ya fitar, firaminista Wen ya bayyana matakai iri daban-daban wajen daidaita matsalolin da ake fuskanta a halin yanzu, ciki kuwa har da ci gaba da aiwatar da manufar kudi cikin himma da kwazo, da kara biyan bukatun abubuwan da jama'a ke saya, da gaggauta kawo sauyi ga hanyar da ake bi wajen neman bunkasuwar tattalin arziki, da daidaita tare da kyautata tsarin tattalin arzikin, da sa kaimi ga bunkasuwar yankuna daban-daban yadda ya kamata da sauransu.

Domin bunkasa tattalin arziki yadda ya kamata, Mista Wen Jiabao ya nuna cewa, kamata ya yi a raya wasu sabbin sana'o'i, da rubanya kokarin bunkasa sabuwar hanyar amfani da makamashi, da sana'o'in da suka shafi yin tsimin makamashi, da kiyaye muhalli, da sadarwa da sauransu. Dadin dadawa, domin tabbatar da bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin mai dorewa, Mista Wen ya ce, ya kamata a daidaita sabani da matsaloli ta hanyar da ta dace, da kuma inganta ra'ayin yaki da matsalar tattalin arziki ta duniya, inda ya ce:

"Ya kamata a kara sa ido kan musanyar kudaden zuba jari tsakanin kasa da kasa, da yin rigakafin abkuwar asarar kudade, da ci gaba da kyautata tsarin tsaida darajar kudin kasar Sin RMB."

Har wa yau, yayin da take ci gaba da kokarin tabbatar da bunkasuwar tattalin arziki yadda ya kamata, gwamnatin kasar Sin tana nan tana kokarin kyautata zaman rayuwar jama'ar kasar. A cikin rahoto kan aikin gwamnati na wannan shekara, an mayar da martani dangane da batutuwan da suka jawo hankalin jama'a sosai, ciki kuwa har da farashin gidaje. A shekarar da ta gabata, farashin gidaje a kasar Sin ya yi tashin-gwauro-zabi, batun da har ya kasance tarihi. Jama'ar kasar Sin suna fatan gwamnatin kasar za ta dauki kwararan matakan rage wannan farashi. A cikin rahoton da ya gabatar, Mista Wen Jiabao ya bayyana cewa:

"Dole ne a taka birki ga hauhawar farashin gidaje a wasu birane, da biya bukatun jama'a na sayen gidajen kwana. Na farko, a ci gaba da kafa gidajen kwana a kokarin bada tabbaci ga inganta rayuwar jama'a. Na biyu, a ci gaba da nuna goyon-baya ga jama'a su sayi gidaje da kansu. Haka kuma, ya kamata a yi kokarin kyautata tsarin kasuwannin kadarorin gidaje."

Kazalika, a cikin wannan rahoto a kan aikin gwamnati, firaminista Wen Jiabao ya bayyana cewa, ya kamata a ci gaba da tafiyar da ayyukan yin gyare-gyare a cikin gida, da bude kofa ga kasashen waje, da inganta harkokin al'adu, da kara yaki da cin hanci da rashawa. Mista Wen ya ce:

"Ya kamata a bada muhimmanci ga batun yaki da cin hanci da rashawa fiye da kome, da kara sa ido kan yadda ake tafiyar da harkokin gwamnati. Ya kamata mu yi kokarin fito da wasu ka'idoji ga jama'a, wajen yin suka kan gwamnati, tare da duba ayyukan da take gudanarwa. Haka kuma, kamata ya yi kafofin watsa labarai su kara taka muhimmiyar rawa."

Game da harkokin diflomasiyya, Mitsa Wen Jiabao ya ce, kasar Sin za ta ci gaba da yin tsayin daka kan aiwatar da manufar diflomasiyya cikin 'yanci, da nacewa ga bin hanyar neman bunkasuwa cikin ruwan sanyi, da yin kokarin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya baki daya.(Murtala)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China