in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kaddamar da taron shekara-shekara na NPC
2010-03-05 09:10:31 cri

A ran 5 ga wata da safe a nan birnin Beijing, an kaddamar da babban taro a karo na uku na majalisa ta 11 ta wakilan jama'ar kasar Sin wato NPC. Hu Jintao da Wu Bangguo da Wen Jiabao da Jia Qinglin da sauran shugabannin jam'iyya da na gwamnatin kasar Sin sun halarci taron.

Shugaban kwamitin dindindin na majalisar NPC Wu Bangguo ya shugabanci taron, a madadin majalisar gudanarwa ta kasar, firaministan kasar Sin Wen Jiabao ya bayar da rahoton aikin gwamnatin kasar ga wakilan jama'ar kasar kimanin dubu 3. Rahoton ya waiwayi ayyukan da gwamnatin kasar Sin ta gudanar a shekarar 2009, kana zai yi shirin ayyukan da za a gudanar a shekarar 2010.

A gun taron kwanaki 9 da rabi, za a saurari da duba rahoton da gwamnati da zaunanen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin da kotun koli da hukumar koli ta bin bahasi ta jama'ar kasar Sin za su yi, sannan kuma za su duba da kuma zartas da shirin bunkasuwar tattalin arziki da zamantakewar al'umma na kasar Sin a shekarar 2010 da shirin kasafin kudin Sin, ban da haka, wakilan majalisar wakilan jama'ar kasar Sin za su duba gyarariyyar dokar zabe.(Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China