in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kira taron 'yan jarida na farko domin taron shekara-shekara na NPC
2010-03-04 17:49:17 cri

Bisa shirin da aka tsara, za a kaddamar da bikin fara taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin a ran 5 ga wata da safe. Sabo da haka, a ran Alhamis, wato ranar 4 ga wata da safe, an kira taron manema labaru na farko na wannan taro, inda Mr. Li Zhaoxing, kakakin taron ya bayyana yadda ake share fagen wannan taro da ajandar taron, har ma ya ba da amsoshi ga tambayoyin da manema labaru na gida da na waje suka yi masa. A gun wannan taron manema labaru, batutuwan yin kwaskwarima kan dokar zabe da yawan kasafin kudin tsaron kasa da manufofin tattalin arziki da kasar Sin za ta dauka sun jawo hankalin 'yan jarida sosai.

Mr. Li Zhaoxing ya ce, za a yi kwanaki 9 da rabi ana tafiyar da wannan babban taron shekara-shekara, wato tun daga ran 5 ga wata da safe zuwa ran 14 ga wata da safe.

Bisa ajandar babban taron, wakilan jama'ar kasar Sin za su tattauna daftarin shirin yin kwaskwarima kan dokar zabe ta kasar. Wannan ne karo na biyar da za a gyara wannan doka bayan an yi gyararta a shekarar 1979. Muhimmin abun da za a gyara shi ne za a zabi wakilan jama'a bisa ma'auni daya a birane da yankunan karkara. Mr. Li ya bayyana cewa, "Yanzu muna da kyakkyawan sharadin zabar wakilan jama'a bisa ma'auni daya a birane da yankunan karkara domin kokarin cimma burin samun daidaito a tsakanin dukkan mutane, kuma a tsakanin yankuna daban daban, kuma a tsakanin kabilu daban daban na kasar."

Li Zhaoxing ya ce, dokar zabe ta kasar Sin da aka kafa a shekarar 1953, tsarin yin zabe ta hanyar dimokuradiyya da aka tsara bisa hakikanin halin da ake ciki a wancan lokacin da ya wuce. Bisa tsohuwar dokar zabe da aka kafa a shekarar 1953, lokacin da ake zabar wakilan jama'a 8 a yankunan karkara, ana iya zabar wakilan jama'a 1 a birane. Sannan a shekarar 1995, an gyara wannan sharadi da cewa, lokacin da ake zabar wakilan jama'a 4 a yankunan karkara, ana iya zabar wakilan jama'a 1 a birane. Yanzu, ana tsammanin cewa, ana da kyakkyawan sharadin zabar wakilan jama'a bisa ma'auni daya a yankunan karkara da birane.

Game da wannan gyare-gyaren da za a yi, Mr. Mo Jihong, shehun malamin da ya kware sosai kan aikin tsara dokokin kasar Sin ya ce, wannan gyare-gyaren da za a yi na da muhimmiyar ma'ana. Ya ce, "Sabon abun da ya fi muhimmanci a cikin sabuwar dokar zabe shi ne za a zabi wakilan jama'a bisa ma'auni daya a yankunan karkara da birane. Irin wannan gyare-gyare za su iya kara kyautata tsarin zabe ta hanyar dimokuradiyya da kimmiya a kasarmu."

Lokacin da yake tabo magana kan yawan kasafin kudin da za a kebe wa aikin soja a kasar Sin, Mr. Li Zhaoxing ya ce, yawan kasafin kudin da za a kebe wa aikin soja a shekarar 2010 zai kai kudin Sin yuan kimanin biliyan 532, wato zai karu da kashi 7.5 cikin dari bisa na bara. Mr. Li ya ce, "A cikin 'yan shekarun nan, yawan kasafin kudin da kasar Sin ta kebe wa aikin soja ya kai kimanin kashi 1.4 cikin dari kawai bisa na jimillar GDP ta kasar, ya yi kadan idan an kwatanta shi da na kasashen Amurka da Britaniya da Faransa da Rasha."

Bugu da kari kuma, batun tattalin arziki shi ne muhimmin batu ne da ke jawo hankalin manema labaru a gun taron manema labarun da aka yi a yau Alhamis a nan Beijing. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China