in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kafofin yada labaru na ketare suna mai da hankali sosai kan tarurrukan NPC da CPPCC
2010-03-04 09:35:52 cri

A yayin da ake yin taron majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta jama'ar kasar Sin da taron majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, kafofin yada labaru na kasashen waje suna mai da hankali sosai kan haka, musamman kan batutuwan tattalin arziki da zaman al'ummar kasar da kuma bunkasa harkokin dimokuradiyya da dai sauransu da za a tattauna.

A ran 3 ga wata, kamfanin dillancin labaru na AP na kasar Amurka ya ba da labari cewa, a shekarar bana, za a mai da hankali kan manufofin tattalin arziki da farashin gidajen zama na birane a gun taruruka biyu na kasar Sin. A sabuwar shekara, gwamnatin kasar Sin tana shirin ci gaba da ba da karin kudi a fannonin ba da ilimi da harkokin tsofaffi, da kuma inshorar jinya, kuma za ta kyautata tsarin ba da tabbacin zaman al'ummar kasar. A sa'a daya kuma, taron majalisar wakilan jama'ar kasar Sin zai bincika shirin gyara dokar zabe.

A ran nan kuma, wata jarida ta kasar Singapore ta ba da sharhi cewa, mambobin majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa da wakilan jama'ar kasar Sin za su mai da hankali kan tattauna batutuwan yin gyare-gyaren tsarin jinya da na ba da ilimi da kuma sauran tsare-tsare. Sharhin ya ce, idan an zartas da shirin gyara dokar zabe, mazauna kauyuka da na birane na kasar Sin za su shiga sabon zamani na samun ikon bisa kada kuri'a. Wannan shi ne muhimmin matakin da za a dauka na bunkasa yunkurin siyasa na dimokuradiyya a kasar Sin.(Asabe)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China