in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Unguwar raya aikin gona da aka kafa a Zhangpu na lardin Fujian domin manoma yankin Taiwan
2010-03-03 21:40:52 cri
Sabo da dukkansu suna shiyyar rashin zafi sosai, birnin Zhangzhou na lardin Fujian da yankin Taiwan suna da sharadin yin hadin gwiwa ta fuskar aikin gona. A shekara ta 2005, an kafa unguwar raya aikin gona ta farko a garin Zhangpu da ke karkarar birnin Zhangzhou domin manoman yankin Taiwan su zuba jari a unguwar.

Mr. Zhang Tangwei, babban direktan kamfanin fasahohin halitta na Zhengyu da ke birnin Zhangzhou, yana daya daga cikin 'yan kasuwa na Taiwan da suka zuba jari a wannan unguwa domin raya aikin gona. Yanzu yana noman furannin Phalaenopsis, wanda wani fure ne mai launin jar garura kuma mai kama da surar malam-bude-littafi a wani sansanin noman furanni da fadinsa ya kai fiye da murabba'in mita dubu 20. Zhang Tangwei ya gaya wa wakilinmu cewa, "Yanayi da ruwa da iska na yankin Zhangzhou dukkansu sun yi daidai da na yankunan tsakiya da na kudancin yankin Taiwan, kuma yana dacewa da noman furanni masu kama da surar malam-bude-littafi sosai."

Manoman yankin Taiwan wadanda suke raya aikin gona a unguwar raya aikin gona ta Zhangpu, sun bayyana cewa, duk da suna zuba dimbin jari da 'yan kwadago da kayayyaki da yawa a wani sabon kamfanin da aka kafa a yankin Taiwan, ba a iya samun moriya kamar yadda ake fata. A yankin Taiwan, babu babbar kasuwar cinikin furanni, amma yawan kudin da ake kashewa domin noman furanni ya yi yawa. A waje daya, a kan samu mahaukaciyar guguwa da bala'un girgizar kasa da sauran bala'u daga indallahi a Taiwan, har ma ko da yake suna da fasahohin zamani wajen noman furanni, amma babu isassun gonaki da kasuwa a Taiwan.

Amma yanayin birnin Zhangzhou ya fi kyau, ba a samu bala'u daga indallahi a kullum a birnin. Sabo da haka, bayan da manoman yankin Taiwan suka zo babban yankin kasar, za su iya raya aikin gona kamar yadda suke fata. Ya zuwa yanzu, galibin manoman yankin Taiwan da suke yin aikin gona a birnin Zhangzhou sun riga sun samu riba. Mr. Zhang Tangwei ya kara da cewa, "Yanzu muna raya harkokinmu kamar yadda mazauna wurin suke yi. Yawan bishiyoyin furannin malam-bude-littafi da muke dasawa ya kai fiye da miliyan 6 a kowace shekara, kuma yawan kudin da muke samu daga wannan sana'a ya kan kai kudin Sin yuan miliyan 20 ko fiye a kowace shekara."

Ban da yanayi mai kyau, yawan kudin da ake kashewa wajen hayar 'yan kwadago a birnin Zhangzhou shi ma kyakkyawan sharadi ne wajen jawo manoman yankin Taiwan da su zuba jari a birnin. Mr. Huang Shengmin, wanda ke tafiyar da wani kamfanin aikin gona a birnin Zhangzhou ya ce, "Yawan kudin hayan 'yan kwadago a wannan wuri kudi ne kadan, wato yawan kudin da muke kashewa ya kai kudin Sin yuan dari 6 ko dari 7 ne kawai a kowane wata a birnin Zhangzhou, amma wannan adadi ya kan kai kudin Sin yuan dubu 3 ko dubu 4 a yankin Taiwan."

An kafa kamfanin da ke karkashin mulkin Huang Shengmin a birnin Zhangzhou ne a shekarar 2007. A cikin shekaru 2 da suka gabata, fadin dakuna masu dumi-dumi na noman bishiyoyin furanni ya kai murabba'in mita dubu 8. Sannan a kwanan baya, wannan kamfani ya sake gina wani daki mai dumi-dumi irin na gilas da fadinsa ya kai murabba'in mita 1200, inda ake nuna ire-iren furanni da kuma sayar da su. Yanzu kamfanin da Huang Shengmin ke tafiya yana nazarin sabbin ire-iren furanni da kuma kokarin raya tamburan furanninsu. Mr. Huang ya kara da cewa, "Kamfaninmu ya kan yi kokarin yada bayanai game da sabon tamburin kayayyakinmu ga masu sayayya. Furannin da masu sayayya suke nuna sha'awa furanni ne da muke kokarin samarwa."

Ya zuwa yanzu, a cikin wannan unguwa, yawan kamfanonin da manoman yankin Taiwan suka kafa ya riga ya kai 70. kuma yawan kudin da suka zuba ya kai dalar Amurka miliyan 120, kuma yawan kudin da aka samar domin kawo arziki ya kai kudin Sin yuan kimanin biliyan 2 a kowace shekara. Mr. He Xihao, shugaban kungiyar 'yan kasuwa na Taiwan wadanda suke aiki a birnin Zhangzhou ya ce, "Yanzu ana iya samun yawancin amfanin gona na Taiwan a birnin Zhangzhou, har ma 'ya'yan itatuwa kamar Lianwu da ake shan wahala sosai wajen noman su."

Mr. Zhang Tangwei, wato shugaban kamfanin fasahohin halitta na Zhengyu, wanda aka gayyace shi da ya zama mataimakin direktan hukumar kula da harkokin wannan unguwa ya bayyana cewa, yana fatan za a iya jawo karin manoman yankin Taiwan dan su zuba jari da kuma samun riba a yankin Zhangzhou. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China