in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude taron majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta jama'ar kasar Sin
2010-03-03 20:06:00 cri
A ranar 3 ga watan Maris da yamma, bisa agogon kasar Sin, an bude babban taron shekara-shekara na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta jama'ar kasar Sin a nan birnin Beijing, wanda ya zama taron a karo na 3 na kwamitin majalisar na 11, inda aka samu halartar bikin bude taron daga wasu shugabannin kasar Sin da na Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin, kamarsu Hu Jintao, da Wu Bangguo, da Wen Jiabao, da Jia Qinglin, da dai sauransu. Sauran 'yan majalisar fiye da 2100 sun halarci bikin.

A wajen bikin da aka yi, Jia Qinglin, shugaban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta jama'ar kasar Sin, ya ba da rahoto kan aikin da zaunannen kwamitin majalisar take yi, inda ya takaita aikin da aka yi a cikin shekarar da ta gabata da cewa, an hada kai sosai, da yi kokarin aiki, ta yadda aka samu babban ci gaba. Sa'an nan, ya bayyana ayyukan majalisar a shekarar 2010 daga fannoni 6.

Abin da aka sa lura a kai shi ne, manyan batutuwa 2 sun zama abubuwan da aka fi baiwa muhimmanci a cikin rahoton da Mista Jia ya bayar, wato su sa kaimi ga samun bunkasuwar tattalin arziki, da kuma kyautata aikin jin dadin jama'a a kasar Sin. Haka kuma, sun kasance manyan ayyukan da majalisar ta yi a shekarar da ta wuce, kana abubuwan da ta fi baiwa muhimmanci a shekarar bana.

A shekarar 2009, sakamakon abkuwar rikicin hada-hadar kudi da ya addabi kasashen duniya, kasar Sin ita ma ta tinkari babban kabubalen da ya haifar da illa ga bunkasuwar tattalin arzikinta. Sa'an nan, majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta jama'ar kasar Sin ta sa kwararrun da suka yi fice a sassan daban daban na al'ummar kasar Sin suka taru, don su ba da shawarwari masu kyau tare da nufin tabbatar da ganin kasar Sin ta samu damar raya tattalin arzikinta da sauri kuma cikin yanayi mai dorewa. Bisa lissafin da aka yi, 'yan majalisar gaba daya sun samar da rahotanni 5820 a shekarar bara, sa'an nan cikinsu 1800 sun shafi aikin tinakarar rikicin kudi da kuma raya tattalin arziki.

Mista Jia Qinglin ya nuna yabo kan aikin da majalisar ta yi, haka kuma, ya bayyana cewa tinkarar rikicin kudi ya zama wata jarrabawa kan gogewar majalisar wajen ba da shawara kan harkokin siyasa, kamar yadda ya fadi cewa, 'Muna mai da hankali sosai kan halin da ake ciki wajen fama da rikicin kudi, da kuma yadda ake gudanar da harkar tattalin arziki a gida. Za mu kara yin bincike, don neman samar da shawarwari masu kyau. Ban da haka kuma, memobin majalisar sun ba da shawarar yin amfani da manufar kudi mai yakini da kuma sassauci da kyau, da yin kokarin habaka bukatun gida, da kuma kiyaye bukatun da aka samu daga kasashen waje. Wadannan shawarwari sun zama abubuwan da Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin da gwamnatin kasar suke dogaro a kai don neman kyautata manufar tattalin arziki ta fuskar manyan tsare-tsare.'

Majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta jama'ar kasar Sin, ba za a iya maye gurbinta ba, ta la'akari da kasancewarta wani tsari mai muhimmanci da ya bayyana dimokuradiyya irin ta zaman gurguzu. Sa'an nan Mista Jia Qinlin ya jaddada cewa, 'Kamata ya yi, a tsara aiki bisa manyan jiguna 2 wato hadin gwiwa da dimokuradiyya, ta yadda za a iya hada karfi daga bangarori daban daban don ba da shawarwari masu kyau.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China