in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tarurrukan majalisu biyu na kasar Sin da za a shirya suna jawo hankula da yawa
2010-03-02 10:01:56 cri

A ran 3 da ran 5 ga wata, a birnin Beijing, za a shirya taron majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta jama'ar kasar Sin da babban taron majalisar wakilan jama'ar kasar Sin bi da bi.

Taro a karo na uku na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta jama'ar kasar Sin a karo na 11 da za a shirya zai shafe kwanaki 10. Menbobin majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta jama'ar kasar Sin fiye da dubu 2 da suke fito daga jam'iyyun siyasa na bangarori daban daban za su ba da shawara da ra'ayoyinsu kan batutuwan da ke dangane da bunkasuwar kasar Sin cikin halin zaman karko da moriyar jama'ar kasar.

Babban taro a karo na uku na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin a karo na 11 da za a bude a ran 5 ga wata zai shafe kwanaki 9 da rabi. mutane kimani 3000 membobin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin za su iso birnin Beijing, don gudanar da aikinsu a madadin dukkan jama'ar kasar Sin. Za su saurari da duba rahoton da gwamnati da kotun koli da hukumar koli ta bin bahasi ta jama'ar kasar Sin da zaunanen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin za su yi, kuma za su duba shirin bunkasuwar tattalin arziki da zamantakewar al'umma na kasar Sin a shekarar 2010 da shirin kasafin kudi na Sin, ban da haka kuma, wakilan majalisar wakilan jama'ar kasar Sin za su duba da kuma zartas da gyarariyyar dokar zabe.Kafin a kammala babban taro a karo na uku na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin a karo na 11, firaministan kasar Sin Wen Jiabao zai gana da manema labaru na Sin da na kasashen waje, kuma zai amsa tambayoyin da ke dangane da batun sauyawar hanyar bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin da ba da tabbaci ga jin dadin jama'a da zaman al'umma da batun sauyawar yanayi da sauransu.(Abubakar)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China