in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Titin Jinli da ke yayata al'adun gargajiya a birnin Chengdu na lardin Sichuan
2010-02-16 17:44:45 cri
Masu karatu, barka da war haka! Tasallah ce ke yi muku marhabin cikin shirinmu na yawon shakatawa a nan kasar Sin daga sashen Hausa na CRI. Yau za mu ci gaba da ziyararmu a lardin Sichuan.

A birnin Chengdu na lardin Sichuan, akwai wani titin yayata al'adun gargajiya da ke da siffar musamman ta wurin, sunansa Jinli. Ana iya kara fahimta kan al'adun gargajiya da mazauna Chengdu suke bi da kuma al'adun gargajiya na lardin Sichuan a wannan waje. Wannan wani shahararren wurin yawon shakatawa ne da ya fi kyau a kai ziyara a lokacin yin yawo a birnin Chengdu. A gabannin bikin Bazara bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin, titin Jinli ya fi kasancewa cike da mutane da hayaniya. Bari mu fahimci kyakkyawan yanayi a can tare. Amma da farko dai za mu yi muku wata tambaya. Yaya titin Jinli da ke birnin Chengdu yake kasancewa? Za ku san amsar bayan da kuka saurari shirinmu na yau!

Titin Jinli na kudancin birnin Chengdu. Tsawonsa ya wuce mita 350. Shi ne titin nishadi da aka gina bisa tsarin gine-gine na gargajiya na kasar Sin. A gefen titin, akwai shaguna da dakunan shan shayi masu benaye 2 ko 3 da aka gina bisa salon gine-gine na gargajiya na kasar Sin, yawancinsu na sayar da kayayyakin gargajiya. In ka shiga ko wani shago, sai fadi-ka-mutu da abubuwan fasaha masu nau'o'i daban daban da aka kera da hannu da ake sayarwa su kan sanya a ji kamar ba a son komawa gida. Yang Ming ya je birnin Chengdu ziyara daga yankin Taiwan ya bayyana cewa,"Yau na yi ziyara a kan titin Jinli. Ina farin ciki sosai. Titin na da siffar musamman ta gargajiya. Ana sayar da kayayyakin gargajiya a nan. Sa'an nan kuma, ana sayar da abinci mai dandano. Abincin da ake sayarwa a nan Chengdu na da dadin ci matuka!"

An gina titin Jinli a dab da gidan ibada na Wuhouci, wato gidan ibada da aka gina domin girmama Zhuge Liang, wani shahararren mai ilmin aikin soja kuma dan siyasa a zamanin Kasashe Uku na tarihin kasa Sin, wato a karni na 3. Wannan titi na matsayin shahararren titin kasuwanci da aka hana zirga-zirgar motoci a kansa a birnin Chengdu. Gong Xian, mai yi wa maziyarta bayani a cibiyar ba da hidimar yawon shakatawa ta titin Jinli ta yi karin bayani da cewa,"Titin Jinli wani titi ne na yayata al'adun gargajiya da ake bi a yammacin lardin Sichuan. Maziyarta daga sassa daban daban na duniya za su kara ilmi kan al'adun gargajiya na wurin. Sa'an nan kuma, mun hada abubuwan da ke shafar tarihin zamanin Kasashe Uku da al'adun gargajiya tare."

Birnin Chengdu ya shahara ne saboda abinci mai dandano. In maziyarta sun je ziyara a wannan birni, idanunsu kan cike da kallon cincin masu nau'o'i daban daban, har ma ba su iya tsai da kuduri kan irin cincin da za su ci. Tare da yin yawo a birnin Chengdu, maziyarta kan iya cika bakinsu da abinci mai dadi, kamshin da ke cika bakinsu ya kan hana su rufe bakinsu

Gong Xian ta yi mana bayani kan wani nau'in cincin mai ban sha'awa da ke da sigar musamman kwarai, sunansa San Da Pao. Tana mai cewa,"Hanyar da ake bi wajen dafa San Da Pao ta sha bamban da saura sosai. A yawancin lokaci, kafin mu shiga dakin cin abinci na sayar da San Da Pao, mun iya jin amo sau 3 da ake samarwa a lokacin da ake dafa shi. Haka kuma, wannan cincin ya samu sunansa ne daga wadannan amon 3. An fito da dunkulen shimkafa mai danko guda 3. Daga baya an jefa wadannan dunkule 3 kan wani katakon tagulla da karfi, ta haka dunkulen su kan fitar da babban amo sau 3. A karshe dai, sai a zuba ruwan bakin sukari da ridi a kansu. Cincin din na da zaki da dandano sosai."

Baya ga dakunan shan shayi na gargajiya da dandamalin nuna wasan kwaikwayon gargajiya, akwai dakunan shan kofi da gidajen nishadi a titin Jinli. An gina da kuma kawatar da wadannan gidajen nishadi ta hanyar muasmman. Su kan nuna sigar musamman ta zamanin yau, amma kusan dukkansu sun bi salon gine-gine na gargajiya da ake kiyayewa a titin Jinli. Ko kusa ba a iya bambance su daga sauran gine-ginen da ake samu a titin Jinli, sun saje sosai da wannan tsohon titi.

Akwai wani fili a tsakiyar titin Jinli, inda aka gina wani dandamalin gargajiya. A kan nuna wasannin gargajiya irin na Sichuan a cikin lokaci kamar yadda aka tsara a kan wannan dandamali mai dogon tarihi. Amma masu yawon shakatawa sun fi son kallon wasannin mutum-mutumi irin na Jinli. Wasannin mutum-mutumi fasaha ce ta gargajiya ta kasar Sin, yau sama da shekaru dubu daya da aka fara yinta. Bayan da masu sana'ar hannu suka yanka fata da alkamashi, suka kuma yi mata ado a tsanake, bayanannun kananan mutum-mutumi da aka yi da fata su kan nuna tarihi. A ko wace rana mutane su kan yi cunkuso a kewayen wuraren da ake nuna wasannin mutum-mutumi a Jinli, musamman ma wadanda suka zo daga kasashen waje, sun fi nuna sha'awa a kan wadannan wasanni. Ga wasu mutane biyu daga kasar Australia."Ni ce Catherine, ni ne Roy. Dukanmu mun zo daga kasar Australia, mun yi minti 10 muna yawo a wannan titi, amma a gaskiya muna son yanayin nan. Jajayen fitilun da aka rataya a dukkan titin na da kyan gani, sun burge mu sosai, mun fi son kallon wasannin mutum-mutumi, Lallai,wannan wani abu ne mai ban sha'awa kwarai a gare mu."

Saboda wasannin mutum-mutumi na samun karbuwa sosai, shi ya sa malam Zhou Yinong, wanda yake nuna irin wannan wasa a titin Jinli, yake jin alfahari kwarai. Ya ce,"Mutane da yawa na gida da na waje da ni mun zama abokai. Wani gidan tebilijin na kasar Italiya ya fito da shirin musamman, inda na koya musu yadda ake yin mutum-mutumin fata da kuma nuna wasan kwaikwayon. Sun koma gida, sun koya wa mutanensu, ta haka sun samu damar fahimtar al'adun kasar Sin. Na yayata al'adun kasar Sin zuwa ketare."

A sakamakon zuwan bikin bazara na shekara ta Damisa bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin, kasaitaccen shagalin gargajiya da a kan yi a birnin Chengdu sau daya a ko wace shekara ya sake zama babban dandamalin da ake iya nuna al'adun gargajiya da ke da sigar musamman ta titin Jinli. A bana, an farashirya wannan kasaitaccen shagali tun daga ran 11 ga wata zuwa ran 3 ga wata mai zuwa a dakin nune-nune na gidan ibada na Wuhouci da ke birnin Chengdu. Ta haka titin Jinli ya zama daya daga cikin muhimman wuraren nune-nune. Madam Gong Xian ta gaya mana cewa,"A titin Jinli, mu kan nuna fasahohin hannu, mun kuma samar da wasu shaguna. Ta haka, maziyarta suna iya ganin abubuwa masu ban sha'awa da wasu abubuwan da masu fasahar hannu suke samarwa kai tsaye a shagalin. Suna iya kallon yadda ake samar da wadannan abubuwa kai tsaye da idonsu. Haka zalika, mu kan nuna wasan kwaikwayo kan al'adun gargajiya."

To, maddala, masu karatu, ziyararmu a titin Jinli a yau ke nan. Kafin mu sa aya ga shirinmu na yau, bari mu maimaita tambayar da muka yi muku a yau. Yaya titin Jinli da ke birnin Chengdu yake kasancewa? Muna jiran amsarku!(Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China