in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kyakkyawan yankin Yanbian da ke kasan babban tsaunin Changbaishan
2010-02-10 11:40:05 cri
Masu karatu, barka da war haka! Tasallah ce ke yi muku "Sannu!" cikin shirinmu na yawon shakatawa a nan kasar Sin. A ko wace ranar Talata mu kan zazzagaya kasar Sin tare. Yankin Yanbian na kabilar Korea mai cin gashin kansa da ke lardin Jilin a arewa maso gabashin kasar Sin na kasancewa bakin iyakar kasashen Sin da Korea ta Arewa da Rasha. Akwai babban tsaunin Changbaishan mai kyan gani kuma mai ban mamaki a wurin, tare kuma da ni'imtattun wurare masu ban mamaki da aka samu a bakin iyakar kasa. Haka kuma, ana iya kara sani kan al'adun gargajiya na 'yan kabilar Korea suke bi. A yankin Yanbian a lokacin hunturu, yin bulaguro tare da kallon dusar kankara ya kara jawo hankalin matafiya matuka. Yau za mu je yankin Yanbian a lardin Jilin domin more ido da kyakkyawar surar wannan wurin da ke arewacin kasar Sin.

A yankin Yanbian da ke lardin Jilin, akwai babban tsaunin Changbaishan, wanda shi ne daya daga cikin shahararrun manyan tsaunuka guda 10 a nan kasar Sin. Wannan shiyyar yawon shakatawa na matakin koli a kasar Sin ya shahara ne saboda tabkin Tianchi da ke bakin dutse mai amon wuta mai ban mamaki da albarkatun dabbobi da tsire-tsire masu yalwa da kuma kyawawan wuraren da dusar kankara ke rufewa. Dimbin bishiyoyi da wurare marasa iyaka da dusar kankara ke mamayewa da magangarar ruwa mai hadari da kuma manyan tabkuna sun samar mana kyan surar wuri mafi kyan gani da ke arewacin kasar Sin. Xu Haoran, wani ma'aikacin cibiyar yayata al'adu ta hukumar harkokin babban tsaunin Changbaishan ya bayyana cewa,"Babban tsaunin Changbaishan ya yi suna sosai a kasar Sin. Yana da kyan gani matuka. Ya kasance daya daga cikin manyan duwatsu masu aman wuta guda 3 a nan kasar Sin da suka taba yin aman wuta a zamanin yanzu. Tsayin kololuwarsa ya kai mita 2691 gaba daya, ta haka ya fi tsayi a arewa maso gabashin kasar Sin. Ina dalilin da ya sa ake kiransa 'Changbaishan', wato babban tsaunin da ke da fari fat har abada? Shi ne duk saboda duwatsu masu fari fat da ke kasancewa a yanayin zafi, kuma a lokacin hunturu, dusar kankara kan rufe babban tsaunin. Babban tsaunin Changbaishan ya dade yana renon 'yan kabilu daban daban a arewa maso gabashin kasar Sin daga zuriya zuwa zuriya, haka kuma, 'yan kabilar Man sun samu asalinsu ne a wajen, dan haka, a zamanin daular Qing, wato a tsakanin shekarar 1636 da ta 1911, sarakuna 'yan kabilar Man sun mayar da babban tsaunin Changbaishan a matsayin babban tsauni mai tsarki."

A lokacin hunturu, babban tsaunin Changbaishan kan nuna kyan siffarsa ta daban. Dusar kankara fari fat da sararin sama mai shudi mai haske da hasken rana sun jawo hankalin masu yawon shakatawa sosai. A da, mutane ba su iya more ido da kyan siffar babban tsaunin a lokacin hunturu ba a sakamakon babbar dusar kankarar da ta rufe babban tsaunin. Amma yanzu na'urorin yawon shakatawa a babban tsaunin sun samu kyautatuwa, mutane suna iya yin bulaguro a wurin a lokacin da aka yi dusar kankara.

Masu karatu, in kun je babban tsaunin Changbaishan ziyara, ya fi kyau ku yi yawo a kewayen tabkin Tianchi. A dab da bakin kololuwar babban tsaunin Changbaishan mai aman wuta, ana samun tabkin Tianchi, shi ne tabki mafi girma kuma mafi tsayi da ke bakin dutse mai aman wuta. A kewayen tabkin, akwai manyan duwatsu da yawa. A cikin tabkin kuma, ruwa mai launin kore na da tsabta. Kogunan Songhuajiang da Tumenjiang da Yalujiang sun samu asalinsu daga wajen wannan tabki, haka kuma, shi ne tabkin da ya raba kasashen Sin da Korea ta Arewa. Xu Haoran ya gaya mana game da asalin tabkin Tianchi da ke da nasaba da wata tatsuniya, inda ya ce,"An ce, matar sarkin sararin sama tana da 'ya'ya 2 mata. Wadannan 'yan mata biyu sun yi kama da juna. Babu wanda zai iya bambance wadda ta fi kyan gani. A yayin wani biki, wani ya ba uwar gidan sararin sama wani madubi kamar wani abun kyauta, wanda ya nuna wadda ta fi kyan gani. Madubin ya ce, karamar ta fi kyan gani. Babbar ta yi fushi, ta jefa madubin daga sararin sama zuwa duniyar 'yan Adam. Madubin ya fada kan babban tsaunin Changbaishan, ya zama tabkin Tianchi."

A gaskiya akwai almara masu ban sha'awa da yawa dangane da tabkin Tianchi. Dukkansu sun sanya tabkin ya kara kyan gani da mamaki, ta haka jama'a da yawa sun yi ziyara a wurin.

Babban tsaunin Changbaishan wani babban dutse mai aman wuta ne da ba a iya barci, ta haka akwai idanun ruwa masu zafi a wurin. Mutane suna iya jin dadi sosai a lokacin da suke kasancewa cikin ruwa mai zafi tare da dusar kankarar da ke yin raye-raye a kewayensu. Xu Haoran ya ce,"Kana iya kasancewa cikin ruwa mai zafi tare da kallon dusar kankarar da ke yin raye-raye a sararin sama da kuma dusar kankara a kewayenka. Dusar kankara ta fada kan fatarka. Kana iya jin sanyi da zafi a lokaci guda. Balle ma more ido da bishiyoyin da dusar kankara ke rufe su a kewayen idanun ruwa masu zafi."

Ana samun jihar Yanbian a bakin iyakar kasashen Sin da Korea ta Arewa da kuma Rasha. Wurin musamman da take kasancewa ya samar da halin musamman ta fuskar al'adun mutane. Shiyyar yawon shakatawa ta Fangfeng a jihar Yanbian tana kudancin birnin Huichun. A wannan shiyyar da ke bakin iyakar kasashen Sin da Rasha da Korea ta Arewa, in kun yi hangen nesa, kuna iya ganin ni'imtattun wurare a kasashen 3. Jin Feng, mataimakin shugaban hukumar harkokin yawon shakatawa ta birnin Huichun ya yi karin bayani da cewa,"Majalisar gudanarwa ta kasar Sin ta amince da shiyyar yawon shakatawa ta Fangfeng a matsayin wurin yawon shakatawa a matakin gwamnatin. Ana samun manyan duwatsu da yawa. A shiyyar dab da manyan duwatsun, akwai koguna da tabkuna. Tana kasancewa a bakin iyakar kasashe guda 3. Wurin musamman da yake kasancewa da yalwar albarkatun namun daji da tsire-tsire sun sanya shiyyar yawon shakatawa ta Fangfeng ta sha bambana da saura."

A jihar kabilar Korea ta Yanbian mai cin gashin kanta da ke kasan babban tsaunin Changbaishan, ana samun 'yan kabilar Korea da yawansu ya kai kashi 80 cikin dari bisa jimillarsu a duk fadin kasar Sin. Wadannan mutane masu ladabi suna son karbar baki da hannu bibbiyu, suna da budaddiyar zuciya. Sun gwanance wajen yin wake-wake da raye-raye, haka kuma, harkokin nishadi da suke gudanarwa sun sha bamban. Yuan Xiaoyun, mataimakiyar shugaban harkokin yawon shakatawa ta jihar Yanbian ta yi mana bayani da cewa, a lokacin da kuke yin ziyara a jihar Yanbian, tabbas ne za ku iya kara fahimta kan al'adun kabilar mabambanta. Tana mai cewa,"Jihar Yanbian kan nuna halin musamman ta fuskar al'adun kabilu sosai. A wannan jiha, duk tufafi da abinci da yare sun sanya mutane su ji kamar yadda suke kasancewa a kasashen waje. Wannan yana da mamaki matuka. Sa'an nan kuma, a shiyyarmu, kana iya more ido da wurare masu ni'imma a kasashe 3. A kan hanyar zuwa babban tsaunin Changbaishan, kana iya ganin dimbin kyawawan bishiyoyin da dusar kankara ke rufewa. Ma iya cewa, jihar Yanbian, wata karamar jiha ce mai matukar kyan gani da tsabta. Tabbas ne kowa zai nuna masa sha'awa kwarai."

A sakamakon bunkasuwar aikin yawon shakatawa, akwai hanyoyi da dama da ke hada jihar Yanbian da wasu wurare. An shimfida hanyoyin jirgin sama da na motoci da hanyoyin dogo a tsakanin Yanbian da sauran biranen kasar Sin da kuma biranen kasashen waje. Haka kuma, akwai isassun ote-otel domin matafiya.

To, masu karatu, jihar Yanbian na maraba da zuwanku domin kara fahimta kan kyan ganin wurin da ke arewancin kasar Sin.(Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China