in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dandana abinci mai dadi a garin Boao na lardin Hainan
2010-02-09 15:06:38 cri
Masu karatu, barka da sabuwar shekara! Tasallah ce ke yi muku marhabin cikin shirinmu na yawon shakatawa a nan kasar Sin. A shekarar da ta gabata, mun zazzagaya tare da ku wasu sassa na nan kasar Sin a ranaikun Talata. Da fatan za ku ci gaba da sauraren shirin da muke gabatar muku. Sinawa kan ce, abinci na gaba da kome ga mutane. A nan Beijing, a halin yanzu ana fama da tsananin sanyi, ta haka a ganina, cika cikinmu da abinci mai dandano yana iya dumamar jiki baki daya. To, yau bari mu je wani karamin garin da ke kudancin kasar Sin. Watakila wasu daga cikinku sun san shi matuka. Madalla, bari mu fara!

A birnin Qionghai da ke tsibirin Hainandao da ke kudancin kasar Sin, akwai wani karamin gari mai suna Boao. Ya shahara sosai a matsayin wurin din din din da a kan shirya taron dandalin tattaunawa kan harkokin Asiya. Baya ga teku da sararin sama masu launin shudi da dogayen bishiyoyin kwakwa da kuma rairayin bakin teku mai kyan gani, garin Boao ya kuma samar wa mutane abinci mai dandano da ke nuna sigar musamman ta wurin.

A cibiyar garin Boao da ake kiransa "garin da ke kamar a aljanna", kana iya dandana abinci mai dadi kuma mai sigar musamman na wurin a shagunan sayar da amfanin teku da aka gina a layi layi. Da farko dai, malama Zhang, wadda ke jagorantar matafiya a wurin ta gabatar mana wata irin miyar da aka dafa da kayan lambu da shinkafa. Ko da yake sunan wannan miya ba shi da dadin ji saboda abubuwan da aka yi amfani da su domin dafa miyar ba su da kyawawan sunaye, amma a ganin malama Zhang, miyar na da dadin ci matuka. Kuma a garin Boao kawai, kana iya dandana wannan miya mai suna Jishiteng Miguozai Tang, wato miyar da aka dafa tare da shinkafa da tsiran Jishiteng, wato Chinese Fevervine Herb a Turance. Tsiran Jishiteng ya samu sunansa ne saboda bayan da aka goge ganye, ganyen kan samar da warin da ya yi kama da kashin kaji, wato Jishi a bakin Sinawa. Inda ta ce,"Jishiteng, wani irin tsiro ne da muke samu a cikin manyan duwatsun da ke dab da kogin Wanquanhe a garinmu. Bayan da aka nika shi zuwa gari, ana hada garin da shinkafa tare, a gauraya su sosai, a nika su zuwa gari, daga baya, a zuba nau'o'in ruwa a cikin garin, a karkasa garin, a samar da kananan kwallaye da yawa, a karshe dai, ana sa wadannan kananan kwallaye da garin sukari da ruwan kwakwa da kuma ruwa tare, mu dafa su yadda ya kamata."

Malama Zhang ta kara da cewa, wannan miya na da zaki da kamshi kwarai da gaske, haka kuma, tana iya kyautata jikin maza da mata duka. A ko wane watan Yuli da na Agusta, a garinta na Boao, kowa da kowa kan sha irin wannan miya.

Baya ga shan miya, kajin da aka dafa tare da ruwan kwakwa na daya daga cikin shahararrun nau'o'in abinci guda 4 a lardin Hainan, a garin Boao kuma, irin wadannan kaji kan sha bamban da wadanda aka dafa a sauran wurare. Malama Zhang ta yi mana karin bayani da cewa, wadanda suke zaune a garin Boao sun yi goman shekaru suna dafa kaji tare da ruwan kwakwa. Wani kukun da ke aiki a gidan abinci mai suna Qiongnan da ke da dogon tarihi a birnin Haikou ya kirkiro wannan abinci. Wannan kuku ya iya dafa abinci ainun, mutane suna nuna masa girmamawa da sonsa sosai, ta haka mutane kan kira shi Qiongnan Sidie, wato tsohon da ke zaune a kudancin Hainan. Yanzu haka dai, ana iya gano reshen wannan tsohon gidan cin abinci a garin Boao. Malama Zhang ta bayyana cewa, tilas ne a yi amfani da kajin Wenchang da mazauna wurin suke kiwo a gidajensu wajen dafa irin wannan abinci. Kajin da mazauna wurin suke kiwo a gidajensu kan ci irin bishiyoyn Banyan a wurin. Dafa irin wannan kaji da ruwan kwakwa tare kan samar da dandano na musamman. Malama Zhang ta ce,"Mu kan zuba ruwa kan kajin Wenchang tare kuma da sanya wasu yankakken citta da tsagaggiyar albasa a kanu, sannan a zuba masu giyar dafa abinci, a turara shi har na tsawon awa guda da rabi. Daga baya, a sa kajin kan faranti. A cikin wata tukunya, mu zuba madara da danyen ruwan kwakwa da sukari da kayan kamshi da kuma sitati tare, a dafa su sosai a wuta, har ma ruwan ya zama mai danko. To, a karshe dai, zuba ruwan mai danko kan kajin ke nan. Irin wannan abinci kan samar da kamshin kwakwa sosai da sosai."

Baya ga abincin da aka dafa da nama, akwai wani nau'in shinkafa da aka dafa da makani. Mutane kan ci kamar yadda su kan ci kayayyakin makulashe. Mazauna lardin Hainan sun dade suna cin irin wannan shinkafa a gidajensu. A garin Boao, matafiya kan dandana irin wannan abinci mai dandano. Malama Zhang ta gaya mana cewa,"Baya ga shinkafa da makani, sai yankakken tuwon cikin kwakwa da dakakkiyar tafarnuwa da yankakken citta ke nan. Mu dafa su tare. Shinkafar na da dadin ci matuka, ta kan samar da kamshin kwakwa da yawa. Bayan ka ci shinkafar, bakinka zai kasance cike yake da kamshin kwakwa."

A sakamakon kasancewarsa a wurin musamman, garin Boao yana da yalwar amfanin teku iri daban daban. Kuryar garin Boao ita ce wurin da shahararren kogin Wanquanhe ya shiga cikin teku. Akwai rairayin bakin teku mai tsawon kilomita 8.5 wai shi Yudai da ake kiran shi a nan, inda matafiya kan kai ziyara. Rairayin bakin teku mai suna Yudai ya raba ruwan kogin da ruwan teku zuwa kashi 2. Ana iya ganin iyakar da ke tsakanin ruwan kogin da na teku a bayyane. In wani ya tsaya a rairayin bakin teku na Yudai, a gabansa akwai igiyar ruwan teku, a bayansa kuma, sai ruwan kogin da ke gangara sannu a hankali. A kusa da rairayin bakin teku na Yudai, akwai wani karamin dakin cin abinci, mai dakin ya gabatar mana shahararrun abincin da dakin cin abincinsa ke samarwa, kuma aka dafa da mabambantan kifaye. Mai dakin cin abincin ya ce,"Garinmu ya yi suna ne saboda yana da yalwar mabambantan kifayen da ke rayuwa a teku. Yawan gishirin da ake samu a wurin da ruwan kogi da ruwan teku suka hadu ba shi da yawa, ta haka kifaye na iya rayuwa yadda ya kamata, namansu na da matukar kyau. Muna da kifaye masu nau'o'i misalin dari 6 gaba daya. Fatarsu na da walkiya da kyan gani, namansu kuma fari fat ne. Ba a iya samun irinsu a sauran wasu sassa."

Kifin Dongxingban, wato Spotted Garoupa a Turance kifi ne na musamman da mai dakin cin abincin ya gabatar mana. Kan irin wannan kifi da kuma wutsiyarsa da aka dafa na da tsada matuka. Ina dalilin da ya sa hakan? Mai dakin cin abincin ya yi mana karin bayani da cewa,"Kansa da kuma jelarsa na da dadin ci kwarai da gaske! Akwai mai da yawa a cikinsu. Kifin kan karkada jelarsa a ko yaushe, ta haka naman da ake samu a jelarsa na da kyau sosai. Kuma naman cikin kifin na da laushi. Naman da ake samu a wadannan bangarori 3 na wannan kifi ya fi tsada."

A wannan karamin dakin cin abinci, ana sayar da wani irin babban jatan lande, wanda ya sha bamban da wadanda muka saba gani a zaman yau da kullum. Sunansa shi ne Squilla. Shi ne amfanin teku na musamman da ake samu a garin Boao kawai. Ba a iya samun irin wannan jatan lande a sauran wurare, sai a wurin da ruwan kogi da ruwan teku suka hadu. Naman irin wannan jatan lande ya fi sauran dadi.

Kasuwa na ci sosai a wannan karamin dakin cin abinci. Mutane da yawa daga sassa daban daban kan shiga da fita, yawancinsu sun sha cin abinci a nan. Wasu su kan je wannan dakin cin abinc ne ta hanyar tuka mota da kansu daga birnin Guangzhou da sauran wurare. Wasu suna zuwa cin abinci a nan daga arewacin kasar Sin. Wannan dakin cin abinci ba ya sayar da abinci mai tsada, dan haka ya samu karbuwa sosai a wurin.

To, masu karatu, ziyararmu a garin Boao a yau ke nan. Ko kuna sha'awar cin abinci a wannan karamin gari? Baya ga taron dandalin tattaunawa kan harkokin Asiya, a wannan karamin gari, kuna iya kallon ni'imtattun wurare da jin dadin zama a wannan garin da ake samu a aljanna kawai, tare kuma da more baki da abinci mai dandano.(Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China