in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kara fahimta kan al'adu mabambanta a birnin Macao
2010-02-09 14:54:40 cri
Masu karatu, barka da war haka! Tasallah ce ke yi muku "Sannu!" a cikin shirinmu na yawon shakatawa a nan kasar Sin. Kamar yadda mu kan yi, yau ma za mu zagaya don yin ziyara a nan kasar Sin tare. A kwanan baya, an yi murnar cika shekaru 10 da mayar da yankin Macao zuwa hannun gwamnatin tsakiya ta kasar Sin. Ko da yake yankin musamman na Macao yana da kankanta, amma kana iya kara fahimta kan abubuwa da yawa a wannan wuri, musamman ma haduwar mabambantan al'adu. Wannan shi ne ra'ayi daya da dimbin mutanen da suka taba zuwa Macao ko kuma suka san shi sosai suka samu.

Masu karatu, a yankin musamman na Macao, in kun bi titin duwatsu da aka shimfida bisa sigar musamman ta kudancin Turai, za ku shiga tsohon bangaren birnin Macao, inda kuke iya ganin coci-coci irin na yammacin duniya da kuma gidajen ibada irin na kasar Sin daya bayan daya. A iyakar karamin titi, ana iya sauraren kide-kiden wasan kwaikwayon gargajiya na Yueju, wato irin wani wasan kwaikwayo ne da aka samo asalinsa a lardin Guangdong na kasar Sin, tare kuma da jin kamshin abinci irin na Guangdong. Kasancewa a cikin irin wannan hali ya kan sanya mutane su ji kamar suna kasancewa a wata farfajiyar nuna mabambantan al'adu."A bangaren dama, muna nuna abubuwan da ke shafar al'adun al'ummar Sin. A bangaren hagu kuwa, ana nuna abubuwan da ke shafar al'adun yammacin duniya, ciki har da babbaku da ilmin falsafa da addinai da kimiyya da fasaha da dai sauransu."

Ga shi Chen Yingxian, shugaban dakin ajiye abubuwan gargajiya na Macao yana mana karin bayani. Ya kuma kara da cewa, yankin Macao ya yi kama da wata farfajiya, inda al'adun gabashin duniya da na yammacin duniya suka hadu, kamar babbakun da Sinawa suka saka a kan kashi ko kuma kashin bayan kunkuru da babbakun gargajiya da mutanen yammacin duniya suka kirkiro, wato Cuneiform, da mutum-mutumin sojoji da dawaki na gargajiya na kasar Sin da jiragen ruwa da 'yan kasar Portugal suka gina a tsakanin shekara ta 476 zuwa ta 1453, da tunanin Lao Zi, wanda ya kirkiro addinin Taoism da ilmin falsafa da Aristotle ya yayata. Ko ina a dakin ajiye abubuwan gargajiya na Macao ya shaida mana kyan haduwar al'adun kasar Sin da na yammacin duniya.

Baya ga al'adu, a dakin ajiye abubuwan gargajiya na Macao, ana iya kara sani kan titunan kasuwanci da ke lardin Guangdong da jihar Guangxi da wuraren da ke makwabtaka da su, da kuma tashar jiragen ruwa ta kasuwanci, inda 'yan kasuwa na sassa daban daban na duniya su kan taru. Sa'an nan kuma, akwai wani titin Macao a wannan dakin ajiye abubuwan gargajiya. A gefunan titin, gidajen mazaunan da ke zaune a lardin Guangdong da wuraren da ke makwabtaka da shi da kuma gidajen da aka gina bisa salon gine-gine na kasar Portugal suna fuskantar da juna. A wasu lokuta, ana iya jin muryar masu tallace-tallace na gargajiya.

A watan Yuli na shekarar 2005, a yayin taron kwamitin abubuwan tarihi na kasa da kasa a karo na 25 na hukumar tarbiya da kimiyya da al'adu ta Majalisar Dinkin Duniya wato UNNESCO, an kudurai aniyar shigar da birnin Macao cikin jerin sunayen abubuwan tarihi na kasa da kasa a matsayin abun tarihi na al'adu na duniya, ta haka birnin Macao ya zama abun tarihi na al'adu na duniya na 31 a nan kasar Sin. Joa'o Manuel Costa Antunes, shugaban hukumar yawon shakatawa ta yankin musamman na Macao ya bayyana cewa,"Birnin Macao shi ne wurin tarihi na tsawon shekaru dari 4 ko fiye da al'adun kasar Sin da na yammacin duniya suka hadu a nan, ya nuna halin musammanmu."

Wuraren tarihi na al'adu da aka samu a Macao sun zama muhimman wuraren yawon shakatawa da matafiya kan kai musu ziyara. Wadannan gine-gine da aka yi su bisa mabambantan salon gine-gine na Sin da na waje a zamanin da da na yanzu, kuma ske amfani da su a fannoni daban daban, sun nuna halin musamman mabambanta sun samar wa Macao sigar musamman ta fuskar al'adu. A wannan karamar Macao, mabambantan al'adu sun hadu, suna kuma bude wa juna zuciya tare da samun bunkasuwa.

Kafin yankin Macao ya koma hannun gwamnatin tsakiya ta kasar Sin, bai lura da haduwar mabambantan al'adu a wurin ba. Amma bayan da aka shigar da yankin Macao cikin jerin sunayen abubuwan tarihi na al'adu na duniya, mazauna Macao da yawa sun fara sanya tunanin darajanta birnin da suke zaune a ciki.

He Lizuan tana aiki a hukumar harkokin al'adu ta Macao. A ganinta, bayan da garinta na Macao ya koma hannun gwamnatin tsakiya ta kasar Sin, ta yi farin ciki matuka a lokacin da take aiki a hukumar harkokin al'adu. A sakamakon kudin da hukumar yankin musamman ta Macao ta zuba kan harkokin al'adu, abokan aikinta da ita suna gudanar da ayyuka yadda ya kamata. Dukkansu sun ga alfanu a fannin aikinsu. Madam He ta ce,"Mun iya takaita abubuwan da suka faru a cikin wadannan shekaru 10 da yankin Macao ya koma hannun gwamnatin tsakiya ta kasar Sin kamar haka: muna kare wannan abun tarihin na al'adu na duniya mai kyau. Mun gina sansanonin al'adu guda 2 domin bauta wa mazauna Macao, wato sansanin horar da masu fasahar wasan kwaikwayo mai suna cibiyar wasan kwaikwayo da fasaha ta Macao, da kuma dakin ajiye abubuwan gargajiya na al'adu na Macao. Haka kuma, mun samar da tambura guda 4 ta fuskar al'adu domin yayata Macao a duk fadin duniya, kamar shagalin kide-kide na Macao da shagalin fasaha na Macao da kungiyar makida ta Macao da kuma kungiyar makidan gargajiya na kasar Sin ta Macao."

A matsayin wurin da aka samu haduwar al'adun kasar Sin da na yammacin duniya, kada matafiya su manta da kara fahimta kan al'adu a wurin. A dandamalin shahaharrun shagulgulan kide-kide da fasaha da aka yi a Macao, a kan ji dadin kallon wasannin da masu fasaha na babban yankin kasar Sin da na yankin musamman na Macao da sassa daban daban na duniya suka nuna. A duk shekara, a kan shirya irin wadannan shagulgula sau da dama.

Yanzu haka dai, mabambantan al'adu na ci gaba da nuna sigar musamman a Macao. Ajandar da hukumar harkokin yawon shakatawa ta Macao ta tsara kan shagulgulan da yankin Macao ya shirya a shekarar 2009, wadanda tilas ne matafiya su halarta, ta nuna mana cewa, baya ga shagulgulan fasaha da kide-kide na kasa da kasa, Macao kan shirya bukukuwa na gargajiya na kasar Sin da na kasashen yammacin duniya da wasu shagulgulan nishadautarwa. Dukkan wadannan bukukuwa kan jawo hankalin mutane da yawa.

Xiao Men, wani dalibin da ya zo daga yankin musamman na Macao, yana karatu a nan Beijing yana ganin cewa, haduwar mabambantan al'adu a garinsa na Macao za ta kasance sabon abun da zai jawo matafiya a nan gaba. Inda ya ce,"Ina koyon yayata kide-kide, amma na fi son koyon yayata al'adu. A hakika dai, al'adun da ake samu a Macao na da ban sha'awa sosai. Ya kamata mu yayata su ta hanyar da ta dace."

Wannan saurayi ya kuma kara da cewa, burinsa shi ne kawar da duk wata gurguwar fahimta kan Macao ta hanyar yayata al'adu. A wannan karamin birni, baya ga aikin caca, ana iya samun mabambantan al'adu masu ban sha'awa. (Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China