in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babban tsaunin Qianlingshan, babban tsauni mafi tsayi a kudu maso yammacin birnin Beijing
2010-02-09 14:25:44 cri
Masu karatu, barka da war haka! Tasallah ce ke yi muku marhabin a cikin shirinmu na yawon shakatawa a nan kasar Sin. A ko wace ranar Talata, mu kan zagaya kasar Sin tare. A ganin Sinawa, hawan babban tsauni na iya bude idon mutane da kuma faranta rayukansu sosai. A nan birnin Beijing, akwai dimbin masu sha'awar hawan dutse. A yawancin lokaci, babban tsaunin Xiangshan wuri ne mafi samun masu hawa a tsakaninsu. Duk da haka, yau zan jagorance ku mu je sabon wurin da shi ma ya cancanci masu sha'awar hawan dutse, shi ne babban tsaunin Qianlingshan, babban tsauni ne mafi tsayi a kudu maso yammacin birnin Beijing.

An samu wurin yawon shakatawa na babban tsaunin Qianlingshan a garin Wangzuo na gundumar Fengtai a kudu maso yammacin birnin Beijing. Yana da nisan kilomita 30 a tsakaninsa da cibiyar birnin. A wurin yawon shakatawar, kyakkyawar surar manyan duwatsu ta sha bamban da juna. Tsayin babbar kololuwar dutsen Jilefeng ya kai mita 699 gaba daya. Ta fi shahariyyar kololuwar Guijianchou ta babban tsaunin Xiangshan tsayi. Ita ce babbar kololuwa mafi tsayi a kudu maso yammacin Beijing. Wu Jianying, wani mazaunin garin Wangzuo ya yi karin bayani da cewa,"Wurin yawon shakatawa na babban tsaunin Qianlingshan da aka raya shi ta hanyar da ta dace ya kasance wurin hutu mai kyau ga mazauna birnin Beijing. Yana da halayen musamman da yawa. Da farko ya nuna halin musamman na addinin Buddha. An samu jerin kogunan dutse mafi yawa a nan, in an kwatanta da sauran wuraren Beijing. Na biyu kuma, ni'imtattun wurare na da kyan gani sosai a nan. Kuma akwai babban tsauni mafi tsayi a kudu masu gabashin Beijing. Na uku kuma, babban tsaunin na da kyakkyawar sura. Yana dacewa da masu sha'awar hawan dutse matuka."

An bude kofar wurin yawon shakatawa na babban tsaunin Qianlingshan a watan Satumba na shekarar 2007 ga matafiya a hukumance. Ana samun albarkatun halittu masu tarin yawa a nan, ciki har da nau'o'in tsirrai fiye da 270. Ban da wannan kuma, bisa binciken da kwararru suka yi kan wannan wurin yawon shakatawa kai tsaye da kuma kayayyakin tarihi da aka tono, an ce, tsawon tarihin wannan wurin yawon shakatawa ya kai a kalla shekaru 400 ko fiye. Lu Xue, wadda ke jagorantar matafiya a wurin yawon shakatwa na babban tsaunin Qianlingshan ta gaya mana cewa,"Wurin yawon shakatawarmu ya yi fice a fannonin al'adun mutane da ni'imtattun wurare da kuma al'adun addinin Buddha. A lokacin bazara, ana iya ganin furanni, a lokacin zafi, ana iya jin dadin kallon rafuka. A lokacin kaka, ana iya more kallon jajayen ganyaye. A lokacin hunturu fa, kankara mai laushi kan cika idon mutane. Sa'an nan kuma, ana iya samun kogunan dutse da ba mutane suka haka ba, sai ikon Allah ne a babban tsauninmu. A da 'yan Buddha su ne suka haka su domin yin ayyukan faratis. Haka zalika, akwai wasu hasumiyoyin addinin Buddha da aka kafa yau shekaru dari 4 ko fiye da suka wuce. Haka kuma, mun gano wasu manyan duwatsu da aka sassaka abubuwa a kai, wadanda yawancinsu aka sassaka yau shekaru dari 4 ko fiye da suka wuce."

Yanzu an raya babban tsaunin Qianlingshan zuwa sabon wuri ne ga mazauna birnin Beijing da su kan motsa jiki ta hanyar hawan dutse. Madam Lu Xue ta kara da cewa, hanyar da aka shimfida a kan babban tsaunin ba ta da gangare da yawa, saboda haka, ta fi dacewa da mutane wajen motsa jiki ta hanyar hawan duste. Inda ta ce,"Mun shimfida hanyoyi a babban tsauninmu da duwatsun da muka samu a wurin. Hanyoyinmu na da inganci sosai. Tsoffafi ba su gamu da matsala ko kuma hadari ba a lokacin da suke bin irin wadannan hanyoyi. Tsayin babbar kololuwarmu ya kai mita 699. Akwai matakai fiye da 3700 gaba daya daga gindin babban tsaunin zuwa kololuwar."

Wang Xin, mataimakin babban sakataren hadaddiyar kungiyar wasan hawan dutse ta birnin Beijing ya yi karin bayani da cewa, a nan birnin Beijing, mutane da yawa suna sha'awar hawan dutse, amma a da babu manyan duwatsu masu dacewa da yawa gare su. Raya babban tsaunin Qianlingshan ta fuskar aikin yawon shakatawa ya samar wa mazauna birnin Beijing masu sha'awar hawan dutse wani sabon zabi. Yana mai cewar,"A nan Beijing, mutane da yawa suna sha'awar hawan dutse. Bisa kwarya-kwaryar kididdigar da muka yi, an ce, yawansu ya wuce miliyan 2, wato mutane fiye da miliyan 2 su kan hau dutse sau daya a ko wane mako. A da mu kan zabi babban tsaunin Xiangshan, har ma babban tsaunin Xiangshan bai iya karbar karin mutane ba. Ta haka, mun tsara shirin bunkasa babban tsaunin Qianlingshan. Dalilan da suka sa haka su ne da farko a matsayinsa na sabon wurin yawon shakatawa, mun shimfida hanyoyin hawan dutse tare da samar da zangunan hutawa da dama. Na biyu kuma, garin Wangzuo ya bunkasa harkokin nishadi ta hanyar wasannin motsa jiki sosai. Akwai filin wasan Golf da dakunan motsa jiki a nan. Dadin dadawa kuma, akwai wani filin wasan kyautata jikin mutane da kuma tunaninsu wato outward-bound a nan, wanda ya fi kyau a duk birnin Beijing. Yanzu haka dai ana shimfida hanyar hawan dutse da hannu da igiyar karfe da ta zama ta farko a duk fadin Asiya, da kuma wani sansani bisa ma'aunin kasa da kasa."

Babban tsaunin Qianlingshan ya na dab da cibiyar birnin Beijing, haka kuma, akwai sauki wajen zuwa babban tsaunin, ta haka hadaddiyar kungiyar wasan hawan dutse ta birnin Beijing tana nan tana hada kai da hukumar wurin da zummar raya babban tsaunin Qianlingshan zuwa sabon wurin yawon shakatawa, inda aka mayar da motsa jiki ta hanyar hawan dutse a gaba da kome, an kuma gina sauran na'urorin motsa jiki da hutawa tare.

Kyan surar babban tsaunin Qianlingshan ta sha bamban bisa lokuta daban daban. Sa'an nan kuma, a kan shirya gasar hawan dutse da tsintar 'ya'yan itatuwa da sauran harkoki masu ban sha'awa, ta haka masu sha'awar hawan dutse da matafiya da yawa da suka fito daga rukunoni daban daban na zaman al'ummar kasar kan je babban tsaunin ziyara, baki da yawa su ma sun je wajen ziyara. Thomas Forrest, wani dan kasar Canada, ya gaya mana cewa,"Na taba hawan babban tsaunin Xiangshan da na Huangshan da na Taishan. Ina son dukkansu matuka! Ina sha'awar iyo da gudu sosai."

Zhang Wenyu, wani mazauni birnin Beijing, ya riga ya yi ritaya daga aiki. Ya kan motsa jiki a babban tsaunin Qianlingshan tare da shugabantar kungiyar hawan dutse ta tsoffi. Ya yi karin bayani da cewa, matsakaicin shekarun mambobin kungiyarsa sun kai 65 a duniya. Shekarun mafi tsufa sun kai 86 a duniya. Mr. Zhang ya ce,"Wadannan tsofaffi suna jin dadin kallon wurare masu ni'ima tare da motsa jiki ta hanyar hawan dutse. Wannan na amfanawa wajen kiwon lafiyar mutane gami da faranta rayuka."

Ni'imtattun wurare da kuma gine-ginen da ke shafar al'adun mutane, wadanda ake samunsu a babban tsaunin Qianlingshan, suna taimakawa juna sosai. Tabbas ne za a yi farin ciki matuka a sakamakon motsa jiki tare da more ido da ni'imtattun wurare a wannan babban lambun renon tsirrai.

To, maddala, masu karatu, karshen ziyararmu a yau ke nan. Tasallah ce ke yi muku ban kwana daga nan sashen Hausa na CRI.(Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China