in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shahararren titin Deshengsha a birnin Haikou
2010-02-09 13:56:30 cri
Masu karatu, barka da war haka! Tasallah ce ke yi muku marhabin a cikin shirinmu na yawon shakatawa a nan kasar Sin. A ko wace ranar Talata,mu kan zagaya kasar Sin tare. Yau za mu yada zango a birnin Haikou na lardin Hainan, inda akwai rairayin bakin teku da dogayen itatuwan kwakwa da hasken rana da kuma tituna masu tsawon tarihi kimanin dari. A birnin Haikou, ta hanyar bin titin Changdilu mai halin musamman na wurare masu zafi da ke bakin teku, sai kuna iya kama wani mikakken titin da aka gina da kananan duwatsu. A gefensa, akwai gine-ginen da aka gina bisa salon gine-gine na kudu maso gabashin Asiya. Wannan shi ne titin Deshengsha mai tsawon tarihi dari, wanda a birnin Haikou, kusan babu wanda bai san sunansa ba. To, yanzu bari mu fara ziyararmu a wannan titi.

Masu karatu, a lokacin da kuke yin yawo a tsakanin wadannan tsoffin gine-ginen da aka gina a shekaru 1920 zuwa 1930 a titin Deshengsha, tare da sauraren tsoffin labarun da mazauna wurin suka fada kan abubuwan da suka faru a cikin wadannan gine-gine da kuma kallon cunkuson mutanen da suke kaiwa da kawowa a titin, kun yi kama da komawa zamanin da. Har kullum wannan titi mai tsawon tarihi dari ko fiye da ya nuna sauye-sauyen birnin Haikou ya kasance abin da mazauna birnin Haikou suke yin alfahari a kai, kuma yana jawo dimbin matafiya daga sassa daban daban.

Mazauna lardin Hainan kan kira rairayin bakin teku da sunan "Sha". A da titin Deshengsha wata muhimmiyar matsayar jirgin ruwa ce a tashar jiragen ruwa ta birnin Haikou, sannu a hankali, an yi ta fadada shi, a karshe dai an samu titin Deshengsha da muka ga a halin yanzu. Da kyar mutane su fahimci ma'anar sunansa sosai. Mr. Wang Haisheng, wani mazauni birnin Haikou ya gaya mana cewa,"In ana cewa, lardin Hainan na matsayin kurya ce ta kudu a kasarmu, birnin Haikou na kasancewa kuryar arewa ta lardin Hainan, to, titin Deshengsha titi ne da ke kuryar arewa a Haikou. A da in mun tsaya a titin, babu hazo, muna iya ganin abubuwan da suke kasancewa a bakin tekun da ke daura. A waccan lokaci, mutane suna kamun kifi da aza kaya da sauke kaya da sayar da kifi da yin ciniki, kuma jami'ai suna shan aiki a titin."

Matsayin titin Deshengsha ya yi kama da matsayin titin Dongjiaominxiang da aka samu a birnin Beijing ko kuma titin Waitan da ke gefen kogin Huangpujiang a birnin Shanghai. Ya zama wanda ya ga manyan sauye-sauyen da idonsa. A karshen zamanin daular Qing ta kasar Sin wato yau shekaru dari ko fiye, titin Deshengsha ya taba kasancewa wurin da masu kai hare daga kasashen waje suka yi ta rikici domin kwace albarkatun tsibirin Hainandao da kuma sayar da kayayyakinsu.

A shekarar 1931, an gina babban ginin Haikou mafi tsayi a birnin Haikou, wanda mazauna wurin kan kira shi "Wucenglou", wato gini mai benaye 5. Wang Haisheng ya san tsohon labari game da wannan gini, inda ya ce,"A waccan lokaci, ginin Wucenglou ya fi shahara a birnin Haikou. Manyan 'yan kasuwa da yawa kan je wajensa domin tattaunawa da shi a kan harkokin ciniki da samun sabbin abokai. A waccan lokaci, kwana a wannan gini mai benaye 5 tare da shan kofi da giyar da aka saya daga kasashen waje ya kasance abin karramawa."

A farkon karni na 19 da ya gabata, dimbin mazauna Hainan sun kama hanyarsu ta zuwa kudu maso gabashin Asiya. Bayan da suka samu kudi a ketare, sun koma gida, suka gina gidajensu a garinsu. Sun koma Hainan tare da tunanin kasashen kudu maso gabashin Asiya, haka kuma, gine-gine da yawa da aka gina bisa salon gine-gine na kudu maso gabashin Asiya sun bayyana a titin Deshengsha da kuma wuraren da ke dab da shi.

A shekarar 1998, an yi kwaskwarima wa titin Deshengsha zuwa titin kasuwanci da aka hana zirga-zirgar motoci, hukumar birnin Haikou ta zuba kudin Sin yuan miliyan 6 ko fiye wajen kayatar da wannan titi yadda ya kamata. A sakamakon gyarar da aka yi masa, tsawon titin Deshengsha ya kai misalin mita dari 5 gaba daya. Haka kuma, an samar wa matafiya manyan kujeru 20 domin hutawa. Sa'an nan kuma, ana adana tsoffin gine-gine masu benaye 2 ko 3 a gefunan titin.

Yanzu titin Deshengsha ya kasance muhimmiyar kasuwar sayar da tufafi a birnin Haikou, haka kuma, shi muhimmiyar kasuwa ce da 'yan kasuwar suka fito daga mabambantan birane da gundumomi na lardin Hainan su kan sayi tufafi domin sayarwa. A wannan kasuwa, ana samar da tufafi masu salo daban daban, kuma ba su da tsada sosai. Maza da mata, tsoffi da yara, in sun shiga kasuwar, tabbas su kan samu abin da suke so, su kan koma gida tare da kayayyaki da yawa cikin farin ciki matuka. Madam Li, wadda ke zaune a lardin Haikou, ta gaya mana cewa,"Idan kana son ka yi yawo a titin Deshengsha, to, ya fi kyau ka shirya sosai. Saboda a titi ne mai hayaniya da wadata matuka. Ba ka iya kallon dukkan komai da komai a wani lokaci. Watakila kana bukatar hutu kadan, bayan ka zaga a wannan titi. Mai yiwuwa ne za ka so ka sake zuwa a nan gaba. Babu tantama, idan ka sake bin titin, to, za ka gano karin sabbin abubuwa masu kyau, saboda kullum ana samun sauye-sauye a wanann titi. Titin ya sha bamban a ko wace rana. Wannan shi ne kyan gani na musamman da titin Deshengsha yake da shi."

Masu karatu, in ka gaji saboda ka sha yin yawo a titin Deshengsha, to, kana iya shiga cikin shaguna domin dandana cincin da ake samarwa. A titin Deshengsha, wasu suna tura kurayensu domin sayar da cincin da suka yi da ridi da tofu, wato abincin da aka dafa da wake da nama. Kana iya sayen abincin kwano guda daga wajensu cikin sauki. Kamar yadda Sinawa kan ce, in kana da giya mai kyau, to, ba ka damuwar cewa, babu wanda ya san giyar da ke buya a titi. Kana iya samun cincin mafi tsantsar dandano kuma mafi dadin ci a layin Fuxingjie da wuri dab da gidan ibada na Ximiao da ke bayan titin Deshengsha. Ya zuwa yanzu cincin da ake samarwa a wadannan wurare na jawo hankalin mutane sosai da sosai. Ko an yi zance kan sunayen wadannan abinci masu dadin ci, sai an zubar da miyau daga baka. Madam Feng, wadda ta je titin Deshengsha daga birnin Guangzhou ta yi bayanin cewa,"A daidai sakamakon kasancewar al'adun gargajiya da cincin mai dandano da kuma mutane masu kirki da suke kasancewa a tsakanin wadannan tsoffin gine-gine a wannan titi, titin Deshengsha na kara nuna kyan ganinsa na musamman. Wannan kuma shi ne dalilin da ya sa na kan je titin Deshengsha a duk lokacin da na je birnin Haikou."

A halin yanzu, a ko wace maraice, a karkashin hasken fitilun da aka gina a gefen titin Deshengsha, kana iya jin farin ciki sosai a lokacin da kake zauna a babbar kujera a gefen titin tare kuma da kallon mazauna birnin Haikou suna komawa gida bayan sun gama aikinsu.

To, masu karatu, in ka je birnin Haikou ziyara, to, ya fi kyau ka yi yawo a wannan titi na Deshengsha mai tsawon tarihi dari guda ko fiye.

To, karshen shirinmu na yau ke nan. Tasallah ce ke yi muku ban kwana daga nan sashen Hausa na CRI.(Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China