in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Garin Boao na lardin Hainan, gari ne da aka samu tamkar a aljanna
2010-02-09 13:47:35 cri
Masu karatu, barka da war haka! Tasallah ce ke yi muku sallama a cikin shirinmu na yawon shakatawa a nan kasar Sin. A ko wace ranar Talata, mu kan zagaya kasar Sin tare. Yau za mu ci gaba da ziyararmu a lardin Hainan da ke kuryar kudu a nan kasar Sin, inda kuma ake samun hasken rana sosai a halin yanzu, ko da yake a yawancin kasar Sin, ana fama da yanayin sanyi.

Garin Boao na birnin Qionghai na lardin Hainan ya shahara ne a matsayin wurin din din din da ake shirya taron dandalin tattaunawa na Asiya. Yana kasancewa inda kogin Wanquanhe na lardin Hainan da tekun da ke kudancin kasar Sin suka hadu da juna. A nan ake samun mashigar teku mafi cika a duniya, inda kogin ya shiga cikin teku. Haka kuma, ana iya ganin kyan surar manyan tsaunuka da koguna da tabkuna da ma ta teku da ta tsibirai duka a wannan karamin gari tare kuma da jin dadin kallon itatuwa da rairayin bakin teku da 'yan tabkuna masu ruwa mai zafi tare da idon ruwa da duwatsu masu ban mamaki da lambuna. Ina dalilin da ya sa wannan karamin gari mai yawan mutane dubu 10 ko da 'yan kai kawai da ke bakin teku ya jawo hankali sosai? Yau bari mu kai masa ziyara.

A lokacin da ake yin ziyara a garin Boao, da farko cibiyar da a kan shirya taron dandalin tattaunar Asiya a ciki kan jawo hankalin mutane. In an hange ta daga nesa, wannan cibiya ta yi kama da wani babban farin kwanso. Ta cancanci wannan gari na zamani da ke bakin teku matuka. Baya ga cibiyar taro ta kasa da kasa a matakin koli, garin Boao ya kuma kyautata na'urorin da abin ya shafa, ya kafa wasu mabambantan otel-otel da manyan dakuna da kauyukan nishadi da na'urorin nishadi domin shirya taron dandalin tattaunawar Asiya. Ta haka wadanda za su halarci duk wani taron za su ji dadin lokacin hutu.

Baya ga shirya tarurruka, garin Boao da aka mayar da shi tamkar karamin gari a aljanna ya yi suna a duk duniya a sakamakon ni'imtattun wurare da halayen musamman na al'adun gargajiya da zaman rayuwa na rashin hayaniya. A kuryar kudu ta wannan gari, shahararren kogin Wanquanhe ya shiga cikin teku, inda kuma akwai wani wurin da ya cika rairayin baki teku mai suna Yudai mai tsawon kilomita 8.5. Matafiyan da su kan je garin Boao ziyara kan yi yawo a wannan wurin da ya cika rairayin bakin teku. Rairayin bakin teku na Yudai ya raba ruwan kogi da ruwan teku zuwa kashi 2. In ka tsaya a kan rairayin bakin teku, a gabanka, teku ya kan turo igiyar ruwa, a bayanka kuma, ruwan kogin na malala sannu sannu. Madam Zhang, wadda ke jagorantar matafiya a wurin ta gaya mana cewa, rairayin bakin teku na Yudai ya karya matsayin bajinta na duniya na littafin tarihi na Guinness, tana mai cewar,"A lokacin kawowar ruwan teku, fadin rairayin bakin teku na Yudai ya kan kai mita 10, wanda ya karya matsayin bajinta na littafin tarihi na Guinness na duniya. Teku mai launin shudi da sararin sama mai launin shudi sun zama tamkar a hade. Kwararrun da suka fito daga kasashen waje sun mayar da wannan wuri a matsayin mashigar teku mafi cika a duniya, inda kogi ya fada cikin teku."

A gabanka, akwai teku, a bayanka kuma, akwai kogi. In ba ka gaskata ba, to, kana iya dandana igiyar ruwan teku da ke gaba da kai da bakinka, lalle, tana da gishiri. Amma dandanon ruwan da ke cikin kogin da ke bayanka ya yi kama da na ruwan sha, babu gishiri ko kadan.

Mazauna wurin kan tuna wa matafiyan da suka fito daga sauran wurare da yin wanka a cikin 'yan tabkuna masu zafin ruwa tare da idon ruwa. A cikin otel-otel da yawa a wurin, matafiya suna iya shiga cikin 'yan tabkuna masu ruwa mai zafi. Madam Zhang ta yi mana karin bayani kan bambancin da ke tsakanin 'yan tabkuna masu ruwa mai zafi a garin Boao da wadanda ake samu a sauran wurare, inda ta ce,"'Yan tabkuna masu ruwa mai zafi na iya taimakawa wajen kiwon lafiyar mutane. Ba safai a kan iya samun irinsu a sauran sassan duniya ba. Zafin ruwa ya fi digiri 70, kuma ya kasa digiri 90. Ko da yake wasu su kan ji warin sinadarin Sulfur wato farar kasa a lokacin da suke cikin ruwa mai zafi, amma a sakamakon kasancewar kananan sinadarai kamar farar kasa a cikin ruwan, fatan mutane kan samu kyautatuwa sosai bayan da suka yi wanka a cikin wadannan 'yan tabkuna masu ruwa mai zafi."

Madam Zhang ta ci gaba da cewa, kauyen Nanqiang da ke kusa da cibiyar garin Boao, wuri ne mai dacewa ga matafiyan da suke ziyara a garin Boao. Suna iya kara ilminsu kan gidajen mazauna garin Boao mai halin musamman da kuma al'adun gargajiya na wurin. A kauyen Nanqiang da ya fi shahara a duk fadin lardin Hainan, akwai wani tsohon gida da wani mutumin da sunan iyalinsa shi ne Cai ya gina. Wannan tsohon gida ya nuna halin musamman na gargajiya na kasar Sin sosai. A kofarsa, an manna jajayen takardu 2 da aka rubuta rubutattun wakokin gargajiya na kasar Sin a kai. Madam Zhang ta gaya mana cewa,"Fadin wannan tsohon gida ya kai kadada 0.2 gaba daya. Fadin muhimman dakuna ya wuce murabba'in mita 1200. Wani dan kasuwa da ya fito daga kasar Indonesia mai suna Cai Jiasen shi ne ya gina wannan tsohon gida mai siffar tsohuwar tasmahara. Ya hada da manyan dakuna 2 da dakuna na layuka 2 da aka gina a kewayen wadannan manyan dakuna 2. Akwai kofofi fiye da 80 da tagogi fiye da 100 da kuma dakuna fiye da 50 a cikin wannan tsohon gida. Sa'an nan kuma, an gina sassan sa ido da na yin harbi a kewayen gidan, da zummar yin kokarin samar da tsaro a gidan. Tsayin babban zauren na muhimmin babban daki a wannan tsohon gida ya kai mita 8 gaba daya."

A cikin wannan tsohon gidan da Cai Jiasen ya gina, an yi dabe masu kyawawan zane-zane a kasa, ko da yake dogon lokaci ya wuce, amma launin wadannan dabe bai kode ba ko kadan. Dadin dadawa kuma, ana kula da cikakken tsohon gidan yadda ya kamata, siffarsa ba ta canza ba ko kusa. An gina shi ne bisa salon gine-gine na gidajen mazauna lardin Hainan da na garin Boao da kuma na gidajen da ake samu a kudu maso gabashin Asiya. Ana iya jin dadin zama a cikin wannan kyakkyawan gida.

A karamin garin Boao, babu shakka lokaci mafi hayaniya a duk shekara shi ne lokacin da ake shirya taron dandalin tattaunawar Asiya. A wancan lokaci, ba ma kawai fararen hular da suka fito daga sauran wurare su kan yi bulaguro a wannan karamin gari ba, har ma manyan mutane ta fuskar siyasa da suka fito daga sassa daban daban na duniya su ma su kan je garin. Ko da yake babu filin jirgin sama a garin Boao tukuna, amma a matsayin wani mai yawon shakatawa, in kana so ka je garin Boao, to, a saukake kana iya zuwa wannan karamin gari da kafarka. Madam Zhang ta ce,"Bayan da kuka sauka a birnin Haikou cikin jiragen sama, kuna iya zuwa garin Boao daga birnin Haikou cikin manyan motocin al'umma kai tsaye, ko kuma, kuna iya zuwa birnin Qionghai cikin manyan motocin daukar fasinja, daga baya, kuna iya shiga bus-bus zuwa garinmu."

To, masu karatu, ziyararmu a garin Booa ke nan, da fatan kun samu karin ilminku kan wannan karamin garin da a kan shirya taron dandalin tattaunawar Asiya. Muna fatan za ku samu damar kai ziyara a garin Boao na lardin Hainan. Tare da wannan waka mai dadin ji, Tasallah ce ke yi muku ban kwana daga nan sashen Hausa na CRI. Ku kasance lafiya. (Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China