in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Birnin Ruili na lardin Yunnan yana raya sana'ar dutse mai daraja
2010-02-08 10:08:06 cri
"Ku duba, ku duba, mu yi amfani da tocila mu haska cikin wannan dutse, idan haske ya iya ketawa ta cikin wannan dutse. Ya alamanta cewa, wannan dutse yana da inganci sosai. Idan babu tocila, shi ke nan, ba za a iya sanin ingancinsa ba. Idan hasken tocila ya iya ratsawa dutse gaba daya, wannan ne dutse mafi kyau. Yanzu haske ya isa wuri na sulusi na wannan dutse, wannan ma dutse ne mai kyau."

Wanda yake bayyana wa masu yawon bude ido abubuwan da ke cikin dutse mai daraja shi ne Ke Wencong, wani dan kasuwa da ke cinikin duwatsu masu daraja a wani titi na birnin Ruili na lardin Yunnan. A shekaru 90 na karnin da ya gabata, ya bar garinsa da ke lardin Fujian ya je birnin Ruili dake bakin iyakar kasar Sin da kasar Myanmar. Ya zuwa yanzu ya riga ya shahara sosai a birnin Ruili kan ilmin dutse mai daraja.

A titin cinikin duwatsu masu daraja na birnin Ruili, yawan 'yan kasuwa wadanda suke cinikin duwatsu masu daraja kamar yadda Mr. Ke Wencong yake yi ya kai fiye da dubu 2. Kuma yawan mutanen da suke yin sana'o'i dangin duwatsu masu daraja a duk birnin Ruili ya kai fiye da dubu 35. Mr. Ke Wencong, wanda shi ne babban sakataren kungiyar cinikin duwatsu masu daraja ta birnin Ruili ya ce, "Ba a buga haraji sosai a kanmu. Yawan harajin da ake bugawa bai wuce kudin Sin yuan miliyan 4 ba a kowace shekara, amma jimillar kudin cinikin duwatsu masu daraja da ake yi a wannan titi ta kai kudin Sin yuan fiye da biliyan 2. Sabo da haka, wadannan kudin harajin da ake bugawa kudi ne 'yan kadan. Gwamnatin wurin tana kokari sosai wajen nuna goyon bayan wannan sana'a, kuma ba ta mai da hankali kan yawan harajin da ake bugawa kan sana'ar duwatsu masu daraja. Tana mai da hankali kan yadda sana'ar duwatsu masu daraja take taka rawa wajen raya sana'o'in yawon bude ido da otel-otel da ba da hayar taksi da dakunan cin abinci da sauran sana'o'in ba da hidima sabo da dukkansu suna iya samar da dimbin guraban aikin yi."

Ko shakka babu, wani muhimmin dalili daban na bunkasa sana'ar duwatsu masu daraja a birnin Ruili shi ne yanayin birni yake ciki. Birnin Ruili yana makwabtaka da kasar Myanmar inda ake samar da duwatsu masu daraja. Sabo da haka, da akwai saukin samun duwatsu masu daraja, yawan kudin da ake sufuri da sarrafawa shi ma kadan ne. Sakamakon haka, farashin duwatsu masu daraja da ake sarrafawa a birnin Ruili ya fi na sauran wuraren kasar Sin arha. Mr. Zheng Zhenquan, shugaban kungiyar cinikin duwatsu masu daraja ta birnin Ruili ya ce, "Kafin shekarar 1995, yawancin mutanen kasar Myanmar su da kansu ne suke hako duwatsu masu daraja da gatura. Tun daga shekarar 1995, sun soma yin amfani da injuna a kai a kai. Alal misali, na san wani mai kamfani da ke da daruruwan injuna domin hako duwatsu a lokaci daya. Sana'ar hakar duwatsu masu daraja ta taka rawa sosai wajen bunkasa sana'o'in yawon bude ido da sufurin kayayyaki a kasar Myanmar, yawan kudin shiga da mutanen kasar Myanmar suke samu ya samu karuwa."

Mr. Phone Kyaw, wani mutumin kasar Myanmar wanda ya riga ya yi shekaru 20 yana cinikin duwatsu masu daraja a birnin Ruili na kasar Sin ya ce, lokacin da ya zo birnin Ruili na kasar Sin yau shekaru 20 da suka gabata, yana da kudin Sin yuan dubu 10 ne kawai, amma yanzu ya riga ya kafa wasu kantunan cinikin duwatsu masu daraja, har ma ya riga ya sayi gida a birnin Ruili, dukkan iyalansa suna rayuwa tare da shi a birnin. Mr. Phone Kyaw ya ce, "A birnin Ruili, yawan harajin da ake bugawa kan baki 'yan kasuwa ya yi daidai da na 'yan kasuwa na kasar Sin, wato kowane wata kowane dan kasuwa wanda ke cinikin duwatsu masu daraja ya biya kudin Sin yuan dari 1 da 50 kawai. 'Ya'yanmu ma suna iya yin karatu a kasar Sin, kuma ana tsaronmu bisa doka."

Idan ba ka san hanyar tabbatar da ingancin duwatsu masu daraja ba, tabbas ne za ka nuna damuwa da cewa, mai yiyuwa ne za a sayi kayan jabu. Game da irin wannan damuwar da ake nunawa, Mr. Zheng Zhenquan, shugaban kungiyar cinikin duwatsu ta birnin Ruili ya ce, "Mun nemi dukkan mambobinmu da su yi kasuwanci cikin sahihanci. Idan an gano cewa wani daga cikinsu yana sayar da kayan jabu, to, shi ke nan, za a janye takardar izinin yin kasuwanci, kuma za a ci tara." (Sanusi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China