Bisa goron gayyata da shugaban babban bankin kasar Sin Zhou Xiaochuan ya yi masa, Donald Kaberuka ya kai ziyara a kasar Sin a hukumance. Yayin da yake zantawa da wakilinmu a hedkwatar bankin raya Afrika da ke cibiyar birnin Tunisiya, ya jinjina wa dangantakar hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika da kuma hadin gwiwa tsakanin babban bankin kasar Sin da bankin raya kasashen Afrika.
Kaberuka ya bayyana cewa, bayan da kasar Sin ta fara yin hadin gwiwa da asusun raya kasashen Afrika da bankin raya kasashen Afrika a shekarar 1985, kasar Sin ta nuna zakewa wajen karfafa hadin gwiwa da bankin raya kasashen Afrika. Ya ce, muna fatan ci gaba da inganta dangantakar hadin gwiwa ta moriyar juna tare da kasar Sin, da koyon fasahohin samun bunkasuwa da Sin ta samu. Ya ce, yanzu kasar Sin na gudanar da matakan raya hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika cikin himma daga dukkan fannoni.
Yayin da aka tabo maganar tasirin da rikicin kudi na duniya ke baiwa kasashen Afrika, Kaberuka ya bayyana cewa, rikicin kudi na duniya ya kawo matsalar tattalin arziki da matsalar samun bunkasuwa ga kasashen Afrika. Sabo da raguwar yawan kayayyaki da kasashen Afrika ke fitarwa ga kasuwannin duniya da raguwar yawan jarin da kasashen duniya suka saka a kasashen Afrika, yanzu, yawan matsakaicin karuwar tattalin arziki da kasashen Afrika suka samu a ko wace shekara, ya ragu daga kashi 6 cikin 100 watau kafin a fada cikin rikicin kudi na duniya zuwa kashi 2 cikin 100. A sakamakon haka, kokarin taimakawa kasashen Afrika wajen fitar da kayayyaki da jawo masu saka jari da farfado da karuwar tattalin arziki sun zama burin da bankin raya kasashen Afrika ta sa a gabanta. Kaberuka ya yi imani da cewa, bayan da kasuwannin kasashen duniya suka kara samun kayayyaki daga kasashen Afrika, tattalin arzikin Afrika zai tsallake daga rikicin kudi na duniya a shekarar 2010.
Donald Kaberuka dan kasar Rwanda, amma ya girma a kasar Zambia, yayin da aka tabo maganar dangantakar sada zumunci ta gargajiya tsakanin kasashen Afrika da kasar Sin, ya ce, dangantakar sada zumunci tsakanin kasashen Afrika da kasar Sin na da daddaden tarihi, tun da can, kasar Sin ta kan yi hadin gwiwa da kasashen Afrika, misali, hanyoyin jiragen kasa tsakanin Tanzania da Zambia, ba wai aka gina a yau ba, ya gaya wa wakilinmu cewa, ya taba yin ziyara kan hanyoyin jiragen kasa tsakanin kasashen Tanzania da Zambia har sau 2, ya zuwa yanzu, ba zai iya manta da shi ba.
Ya jaddada cewa, hadin gwiwa tsakanin kasashen Afrika da kasar Sin moriyar juna ne, kuma muradu ne na bangarorin biyu. A cikin shekaru 30 da suka shige, dangantakar hadin gwiwa tsakaninsu ta samu bunkasuwa sosai, kana zaman rayuwar Sinawa ta samu kyautatuwa sosai, kuma yawan matalauta a kasar Sin ya ragu sosai, kamata ya yi kasashen Afrika da sauran kasashen duniya su koyi da fasahohin da kasar Sin ta samu.(Bako)