Wannan shi ne karo na farko da aka kafa unguwanni mafi kyau a cikin tarihin bikin baje-koli na duniya, kuma za a nuna unguwannin musamman 50 da kwamitin zabe na duniya ya zaba daga birane 80, cikinsu sun hada da birnin Rotterdam da aka yi masa lakabi da sunan "Birni da ke dagora ga ruwa" da unguwar Tak Seng On a yankin musamman na Macao.
An kafa yankunan nuna unguwanni mafi girma na duniya da fadinsu ya kai kadada 15, cikinsu sun hada da unguwannin kyawawan gidaje da aikin samun bunkasuwar birane cikin dogon lokaci da aikin kiyaye abubuwan tarihi da yin amfani da su da aikin fasahohin zamani da kirkire-kirkire ta fuskar kiyaye muhalli.(Bako)