A cikin wadannan harkoki, shugabannin kungiyoyi kusan 20 na ba da hidima a cikin dakin nune-nune na hadin gwiwar Afirka sun nuna fatansu na gudanar da harkokin nune-nune bisa ajandar ayyuka, ta haka za a iya samar da dakin nune-nune mai kayatarwa.
A yayin taron baje-koli na duniya da za a yi a birnin Shanghai na kasar Sin, kungiyar tarayyar Afirka da kasashe 42 na Afirka za su kasance cikin dakin nune-nune na hadin gwiwar Afirka. Yawansu ya fi yawa a tarihin dakin nune-nune na hadin gwiwar Afirka a yayin taron baje-koli na duniya.
Haka kuma, dakin nune-nune na hadin gwiwar Afirka dakin nune-nune ne mafi girma a cikin dukkan dakunan nune-nune na hadin gwiwa a dandalin taron baje-koli na duniya na Shanghai. Yanzu ana yi masa ado da kuma gudanar da harkokin nune-nune cikin himma da kwazo.(Tasallah)