Katin Yinlian, wani katin kudi ne da yake kasancewa tamkar katin Master da katin Visa da ake amfani da su a duk fadin duniya domin daidaita harkokin kudi cikin sauri.
An bayar da labari cewa, an yi hasashen cewa, 'yan kasuwa fiye da dubu 3 za su iya yin amfani da katin Yinlian domin daidaita harkokin kudi a kan injunan ATM a cikin shekarar da ake ciki. (Sanusi Chen)