A cikin shirinmu na yau, bari mu fara duba wani labari da muka samu daga jaridar The New Times ta kasar Ruwanda, wadda aka buga a ran 20 ga wata, inda aka bayyana cewa, kasar Libya za ta kara zuba jari a Ruwanda.
Jaridar the New Times ta kasar Ruwanda ta bayyana cewa, kamfanin gwamnatin kasar Libya wato LAP yana son kara zuba jari mai yawan gaske a fannin tattalin arzikin Ruwanda.
Darektan hukumar da ke kula da harkokin raya Ruwanda mista John Gara ya sanar da cewa, kasar Libiya tana fatan kara neman damar yin cinikayya a fannonin hakar ma'adinai, da aikin gona, da gidajen kwana da yawon shakatawa da dai sauransu.
Kamfanin LAP na kasar Libiya ya riga ya zuba jari a fannonin sadarwa ta wayar iska, da kuma otel-otel, har ya riga ya sarrafa hannun jari na kamfanin sadarwa na Ruwanda wato Ruwandatel SA da kuma kamfanin otel na Laico Umubano Hotel.
Mista Gara ya kara da cewa, mai yiyuwa ne kasar Libiya za ta kara zuba jari a kasar Ruwanda, sabo da tana son kara samun dama a Ruwanda.
Wata tawagar kamfanin LAP ta isa Ruwanda a ran 18 ga wata, domin kiddigar ayyukan da suka zuba jari kansu da kuma neman sabuwar dama wajen yin cinikayya.
Mataimakin shugaban kamfanin LAP mista Khaled Kagigi, wanda ya shugabanci wannan tawaga ya bayyana cewa, kamfanin LAP yana shirin gina gidajen kwana da yawansu zai kai 400 a Ruwanda. Ya ce,
Za a fara wannan aiki a nan gaba ba da dadewa ba cikin hadin gwiwar kamfanin sadarwa na Ruwanda wato Ruwandatel da kamfanin gine-gine na LAP. Kagigi ya kara da cewa, dalilin da ya sa kamfanin LAP ya zuba jari a fannin gina gidaje ne shi ne, domin a ganinsa wannan fanni yana da wata kyakkyawar makoma.
A yayin da tawagar take ziyara a Ruwanda na tsawon kwanaki 3, mambobin tawagar sun gana da firayin minista Bernard Makuza, da kuma ministan da ke kula da harkokin kudi da harkokin waje, da kuma shugabannin a kamfanin Ruwandatel SA da kuma kamfanin otel na Laico Umubano Hotel.
Jama'a masu karatu, bayan haka kuma bari sake duba wani bayani da muka samu daga kamfanin labaru na IRIN na MDD da ke a nahiyar Afirka, wanda aka fitar a ran 19 ga wata, inda aka bayyana cewa, mai yiyuwa ne kasar Swaziland za ta kara ba da tallafin kudi ga manoma domin daidaita matsalar karancin hatsi da ake samu a kasar.
Kamfanin watsa labaru na MDD wato IRIN da ke a Afirka ya bayyana cewa, kasar Swaziland tana shirin kara ba da tallafin kudi a fannin aikin gona, domin kara samun hatsi a wannan kasa, wadda take fama da matsalar karancin abinci.
Amma ya kamata majalisar dokoki ta zartas da wannan shiri da farko, sa'an nan kuma za a iya kafa wani asusu da ke zuba kudade ga aikin gona kafin lokacin damina a watan Oktoba.
A cikin shekaru fiye da goma da suka gabata, kashi 66 daga cikin dari na jama'ar Swaziland suna dogaro da kyautar abinci da ake ba su, sabo da babu isashen hatsi da aka iya samu bisa ga karancin ruwan samo a kasar. A shekarar 2009, an yi ruwan sama da ya fi na da yawa, amma wannan bai taimaka sosai ba wajen daidaita matsalar karancin hatsi da aka samu a kasar.
Dalilin da ya sa gwamnatin Swaziland take son ba da tallafin kudi ga aikin gona shi ne, domin yana son koyi da kasar Mawali, wadda ta gudanar da manufar ba da tallafi kudi ga manoma a shekarar 2009, ban da wannan kuma Mawali ta samu ruwan sama mai yawa a shekarar 2009, sakamakon wadannan dalilai biyu da muka ambata, kasar Malawi ta samu masara da yawanta ya kai ton miliyan 3.77 a shekarar 2009.(Danladi)