
Tun daga ran 11 zuwa ran 17 ga wata, a karkashin jagorancin Chen Deming, tawagar tattalin arziki da cinikayya ta gwamnatin kasar Sin ta kai ziyara a kasashe 3 na Afirka wato Habasha da Mozambique da Tanzania. Bisa labarin da jaridar People's Daily ta kasar Sin ta bayar a ran 20 ga wata, an ce, Chen Deming ya bayyana wa manema labaru cewa, a 'yan shekaru da suka wuce, bisa kasar Sin ta kara yin hadin gwiwa tare da kasashen Afirka a fannin ciniki, an yi zargi cewar kasar Sin ta aiwatar da sabon mulkin mallaka, amma wannan bai dace da hali ba. Ya kara da cewa, kamfanonin kasar Sin sun shiga ayyukan bunkasa kasashen Afirka ta hanyar yin takara cikin adalci, kuma sun kara samar da guraben ayyukan da ba da taimako ga kasashen Afirka wajen tallafa kudi.(Abubakar)




