in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Aikin gyara tsoffin gidajen kwana da ake yi yana moriyar jama'a
2010-01-19 20:13:51 cri
Gandun daji muhimmin shingen tabbatar da yanayi mai daukar sauti, kuma muhimmin sansani ne da ke samar da katako a arewacin kasar Sin. Bayan kafuwar sabuwar kasar Sin, lokacin da ake raya gandun daji, sabo da an sanya aikin kawo arziki a gaban kome, ba a samar da ayyukan yau da kullum kamar yadda ya kamata a gandun daji, sakamakon haka, ma'aikata ba su da gidajen kwana masu inganci. Tun daga shekarar 2009, kasar Sin ta kaddamar da ayyukan gyara tsoffin gidaje marasa inganci a wasu gandunan daji da ke hannun gwamnati. Bisa shirin da aka tsara, za a yi amfani da shekaru 3 wajen gyara gidajen kwana da fadinsu zai kai fiye da murabba'in mita miliyan 1 a yankin Daxing'anlin na jihar Mongoliya ta gida, wato na daya daga cikin manyan gandunan daji da ke arewacin kasar Sin. Sakamakon haka, za a iya daidaita matsalar rashin gidaje masu inganci da iyalai fiye da dubu 10 suke fuskanta. A cikin shirinmu na yau, za mu karanta muku wani bayani game da yadda ake yin wannan aiki.

A ran 8 ga watan Satumba na shekarar 2009, saurayi Ma Rui da amaryarsa Li Mei wadanda suke aiki a hukumar kula da gandun daji na Daxing'anlin sun shiga wani sabon gida lokacin da aka shirya musu bikin aure. Kafin su yi aure, Ma Rui ya yi zama a wani tsohon gidan da aka gina da katako da duwatsu, kuma iyayensa sun ba shi. Wannan tsohon gida ba shi da inganci. Sabo da haka, Ma Rui ya ji farin ciki sosai shi da amaryarsa sun iya shiga sabon gida. Ma Rui ya ce, "Ina farin ciki kwarai. Ban iya bayyana irin wannan farin ciki da maganganu ba. A takaice dai, ina farin ciki. Kuma na ji na samu sa'a. Na gode wa dukkan wadanda suke kula da mu."

Ma Rui da matansa su ne daya daga cikin iyalai 500 da suka samu sabbin gidajen da hukumar kula da gandun daji ta Mangui da ke jihar Mongoliya ta gida ta gina a shekarar 2009. A shekarar 2009, wannan hukuma ta gina sabbin gine-gine 12. Yanzu an riga an gama aikin gina su duka. Wadannan gine-gine su ma daya daga cikin aikin samar da sabbin gidajen da ake yi a babban gandun daji na Daxing'anlin na jihar Mongoliya ta gida.

Bisa kididdigar da hukumar kula da harkokin gandun daji ta Daxing'anlin ta jihar Mongoliya ta gida ta yi, an ce, yawan iyalan da suke kwana a cikin tsoffin gidaje marasa inganci ya kai kimanin dubu 77, kuma fadin irin wadannan gidaje ya kai murabba'in mita miliyan 3, wato ya kai kashi fiye da kashi 53 cikin dari bisa jimillar gidajen hukumar.

Yanzu batun karancin gidaje masu inganci da ke kasancewa a gaban jama'a ya jawo hankalin gwamnatin tsakiya da gwamnatocin matakai daban daban. A shekarar 2009, hukumar kula da harkokin gandun daji ta Daxing'anlin ta yi kokarin kebe kudin da yawansa ya kai kudin Sin yuan biliyan 1 da miliyan dari 3 domin kyautata tsoffin gidajen da fadinsu ya kai murabba'in mita miliyan 1. Mr. Zhang Xueqin wanda ke jagorancin hukumar ya ce, "Ya zuwa karshen shekarar 2009, mun riga mun gama aikin gyara gidajen da fadinsu ya kai murabba'in mita dubu 750. Sabo da haka, iyalai kimanin dubu 15 sun shiga sabbin gidaje masu inganci. Muna fatan dukkan ma'aikatanmu za su iya shiga sabbin gidaje, kuma za a iya kyautata zaman rayuwarsu kamar yadda ake fata."

Mr. Zhao Baojun, mataimakin babban direktan kamfanin raya gandun daji na jihar Mongoliya ta gida ya ce, yanzu ana ci gaba da aikin gyara tsoffin gidaje bisa shirin da aka tsara. Ya kara da cewa, ba ma kawai wannan aiki ya taka rawa wajen kyautata gidaje ba, har ma ya taka rawa sosai wajen raya tattalin arzikin wurin. Ya ce, "Yawan kudin da gwamnatin tsakiya ta zuba ya kai kudin Sin yuan miliyan 320, wannan ya sa sauran bangarori da su zuba kudin da yawansa ya kai kudin Sin yuan biliyan 1 da miliyan dari 2. Wadannan kudaden da aka zuba sun zama muhimmin karfi wajen ci gaban tattalin arziki. A waje daya, an samar da wasu guraban aikin yi lokacin da ake gyara tsoffin gidajen da suke cikin hadari. Sabo da haka, an ce, ba ma kawai wannan matakin gyara tsoffin gidajen da suke cikin hadari ya iya taka rawa wajen raya tattalin arziki ba, har ma yana iya taka rawa wajen kyautata ingancin zaman rayuwar bayin Allah." (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China