in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An shiga matakin karshe na share fagen taron baje-koli na duniya na Shanghai
2010-01-18 19:21:25 cri
Yau ya rage sauran kwanaki 103 a bude taron baje-koli na duniya na Shanghai, bayan da aka share fagen taron a tsanake har na tsawon shekaru 7. Ran 18 ga wata, ofishin watsa labaru na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya shirya taron manema labaru a nan Beijing, inda Yang Xiong, mataimakin magajin birnin Shanghai mai kula da harkokin yau da kullum kuma mataimakin darektan kula da harkokin yau da kullum na kwamitin zartaswa na taron baje koli na duniya na Shanghai ya bayyana cewa, yanzu an shiga matakin karshe na share fagen taron. Yawan sassan duniya da za su shiga taron zai sauya matsayinsa a tarihi.

Mr. Yang ya yi karin bayani da cewa, yanzu kasashe 192 da kungiyoyin kasa da kasa 50 sun tabbatar da aniyar shiga taron, yayin da larduna da jihohi da birane 31 da Hong Kong da Macao da Taiwan na kasar Sin su ma za su shiga taron. Inda ya ce,"An kusa kawo karshen gina dakunan nune-nune. An kaddamar da ayyukan nune-nune daga dukkan fannoni. Ban da wannan kuma, an kusa kammala gina farfajiyar taron baje koli na duniya. An kammala gina dakin nuna babban taken taron da cibiyar taron baje-koli na duniya, yayin da aka kusa kammala gina dakin kasar Sin da cibiyar nuna wasanni da wani muhimmin gini na daban wato Expo Axis. A yayin taron, kasashe 42 sun gina dakunansu, yayin da aka gina dakunan masana'antu guda 18, wadanda yawancinsu aka fara yi musu ado da gudanar da ayyukan nune-nune, saura kuma, ana gaggauta ayyukan kammala su da yin shirin kaddamar da nune-nune. Sa'an nan kuma, an riga an gama gina dukkan dakunan nune-nune 42 na yin haya da dakunan nune-nune na hadin gwiwa 11. Za a mika su ga hannun wadanda za su shiga taron domin fara ayyukan nune-nune."

Yanzu ana share fagen tafiyar da harkokin taron baje-koli na duniya na Shanghai daga dukkan fannoni. Shanghai ta riga ta kaddamar da shirin zirga-zirga a yayin da ake yin taron baje-koli na duniya. Mr. Yang ya yi bayani da cewa,"Muna daukar matakai da yawa domin samar wa matafiya sauki. Akwai hanyoyi 5 na jiragen kasa da ke karkashin kasa da ke ratsawa farfajiyar taron baje-koli na duniya, ko kuma suke wucewa ta wuraren da ke makwabtaka da farfajiyar. Mun kuma samar da motoci kusan dubu guda da ke zuwa farfajiyar kai tsaye, yayin da hanyoyin motocin al'umma fiye da 90 suka ratsa farfajiyar. Idan mutane kimanin dubu 400 ne suka kai ziyara a farfajiyar a ko wace rana, to, za mu iya biyan bukatunsu, amma watakila a wasu lokuta, za a samu cunkuson motoci a wasu wurare."

Game da aikin tsaro, mai kula da harkokin shirya taron baje-koli na duniya na Shanghai ya nuna cewa, za a dauki muhimman matakan tsaro masu dacewa domin tabbatar da ganin an shirya taron baje-koli na duniya cikin kwanciyar hankali da farin ciki.

A sakamakon kusantowar ranar bude taron baje-koli na duniya, ana samun kyakkyawan yanayi a birnin na Shanghai. A ko ina a wannan birni, ana iya ganin abubuwan da ke da nufin yayata taron. An kuma kayatar da shahararrun wuraren yawon shakatawa da yawa, tare da yi musu kwaskwarima. Haka zalika, masu aikin sa kai sun riga sun fara ba da hidima. Mazauna wurin su ma suna shiga ayyukan shirya taron cikin himma da kwazo. Suna Alla-Alla wajen koyon Turanci da sauran fannonin ilmi dangane da taron baje-koli na duniya. Chen Xiangrong, wanda ke zaune a birnin Shanghai ya bayyana cewa,"A matsayina na wanda ke zaune a birnin Shanghai, ko wanenmu yana farin ciki matuka saboda taron baje-koli na duniya. Ya kamata kowa ya ba da gudummawarsa. Ina alfaharin shiga cikin ayyukan shirya taron."(Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China