in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Algeria ya gana da Yang Jiechi
2010-01-11 22:24:38 cri

A ran 10 ga wata a birnin Algiers, babban birnin kasar Algeria, shugaban kasar Abddaziz Bouteflika ya gana da ministan harkokin waje na kasar Sin Yang Jiechi da ke ziyara a kasar.

Yang Jiechi ya ce, a cikin shekaru 51 da aka kafa dangantakar diplomasiyya dake tsakanin Sin da Algeria, kasashen biyu da jama'arsu sun nuna goyon baya da juna da fahimtar juna da yin hadin gwiwa tsakaninsu, kana sun inganta hadin gwiwarsu a karkashin tsarin dandalin tattaunawa kan hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka da kasashen Larabawa. Sin ta dora muhimmanci kan zumunta tsakaninta da Algeria, kana tana son yin kokari tare da kasar Algeria wajen kara yin mu'amala da fadada hadin gwiwa don inganta dangantakar hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare tsakaninsu zuwa wani sabon matsayi.

Mr Bouteflika ya bayyana cewa, kasar Algeria ita ce abokiyar kasar Sin, dangantaka tsakaninsu ita ce dangantakar abokantaka ta musamman. Kasar Algeria tana son yin kokari tare da kasar Sin wajen inganta dangantakar hadin gwiwa tsakaninsu. Kasar Algeria ta tsaya tsayin daka kan manufar Sin daya tak, da nuna goyon baya ga babban sha'anin samun dinkuwar kasar Sin baki daya.

Mr Bouteflika ya ce, dandalin tattaunawa kan hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka da kasashen Larabawa ya ba da taimako wajen inganta hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka da kasashen Larabawa, kasar Algeria tana son sa kaimi ga dangantaka tsakanin Sin da kasashen Afirka da kasashen Larabawa da ta samu ci gaba.(Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China