in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bayan ruwan sama da iska, sai bakan gizo
2010-01-11 14:54:19 cri
Bayan da ya karanta jadawalin sakamakon da kamfaninsa ya samu, Mr. Chen Haixian ya saki jikinsa ya ce, "Yanzu kamfaninmu ya soma koma hanya madaidaiciya wajen kawo arziki da sayar da kayayyaki sabo da yana fita daga mawuyacin halin da ake ciki sakamakon rikicin kudi na duniya a kai a kai. Bisa kididdigar da muka yi, an ce, yawan kudin da muka samu bayan da muka sayar da kayayyakinmu da jimillar kayayyakin da muka samar sun ragu sakamakon wannan rikicin kudi. Amma mun kuma samu karuwa a wasu fannoni lokacin da muke fama da rikicin. Sabo da haka, a takaice dai, matsayin da kamfaninmu ya dauka a shekarar 2009 ya yi daidai da na shekarar 2008."

Mr. Chen Haixian, mai shekaru 48 da haihuwa, shugaba ne na wani kamfanin cinikin waje na lardin Zhejiang ya riga ya yi shekaru da yawa yana yin wannan aiki. A tsakiyar shekaru 90 na karnin da ya gabata, Chen Haixian ya yi murabus daga wani kamfanin gwamnati, ya kafa kamfanin sarrafa sinadarai mai suna Bakan Gizo. A cikin shekaru fiye da 10 da suka gabata, kamfanin Bakan Gizo da yawan ma'aikatansa ya kai dari 5 ya zama wani matsakaicin kamfani, kuma ya zama rukunin kamfanoni na Bakan Gizo, inda ake samar da danyun kayayyaki na yin takalma. Kuma yana sayar da rabin kayayyaki zuwa kamfanonin yin takalma da ke lardunan Zhejiang da Jiangsu, sannan yana sayar da sauran rabi zuwa kasashen waje. A da, yana samun riba kwarai, amma a yanayin rikicin hada-hadar kudi da ya bullo ba zato ba tsammani, kamfanin Bakan Gizo da Mr. Chen Haixian sun fuskanci matsin lambar da ba su samu ba a da. Chen Haixian ya gaya wa wakilinmu cewa, "A lokacin da rikicin hada-hadar kudi na duniya ya auku, yawan kwangilolin da muke samu ya ragu da kimanin kashi 30 cikin dari. A waje daya, ba mu iya samun kudin da ya kamata a mayar mana ba. Amma yawan kudin da muke kashewa domin tafiyar da kamfaninmu ya karu sosai."

Karfin raya tattalin arziki da kasuwanni na kasashen Amurka da Turai da Japan ya ragu sakamakon wannan rikicin hada-hadar kudi na duniya. Wadannan yankuna muhimman kasuwanni ne ga kamfanin Bakan Gizo. Chen Haixian ya ce, wannan rikicin hada-hadar kudi na duniya ya bullo kamar irin yadda a kan gamu da dusar kankara mai tsanani sosai ba zato ba tsammani. Kamfanonin cinikin waje da yawa sun yi sanyi kwarai. Mr. Chen Haixian ya ce, "Dimbin baki na kasashen waje sun soke kwangiloli. Kamfanonin yin takalma da yawa sun kuma dakatar da yin takalma sakamakon karancin kwangiloli, har ma wasu daga cikinsu sun sallami ma'aikata. Wasu kamfanoni ba su da isasshen kudin gudanar da ayyukansu. Sannan an rufe wasu kamfanoni sakamakon gushewar imani."

Wasu sassan yin kayayyaki na kamfanin Bakan Gizo sun dakatar da yin aiki sakamakon karancin isassun kwangiloli. Ma'aikatan kamfanin ba su saba da irin wannan halin da suke ciki ba. Mr. Li Jianli wanda ya yi shekaru 10 da wani abu yana aiki a kamfanin Bakan Gizo ya ce, a da, dukkan injuna da na'urori na kamfanin suna aiki ba dare ba rana, amma wannan rikicin hada-hadar kudi na duniya ya canja irin wannan yanayi. Li Jianli ya ce, "Bayan aukuwar rikicin hada-hadar kudi na duniya, a bayyane ne yawan kwangiloli ya ragu, aikin da ke rataye a wuyanmu ma ya ragu sosai. A wasu lokuta, mu kan dakatar da aikinmu. A da, tsawon lokacin aikinmu na kowace rana shi ne sa'o'i 8, amma, yanzu bai wuce sa'o'i uku ko hudu ba. Muna hutu a sauran lokuta. A wancan lokaci, yawan injunan da ba sa aiki ba su wuce biyu bisa uku ba."

Amma abin da Li Jianli ya nuna damuwa shi ne mai yiyuwa ne wata rana za a sallame shi. Li Jianli ya ce, "Lokacin da kamfanin yake cikin mawuyacin hali sosai, na damu sosai. Na gaya wa iyalina cewa, mai yiyuwa ne zan rasa gurbin aikin yi, har ma wasu lokuta ba na iya yin barci. Kusan dukkan ma'aikata sun nuna damuwa a wancan lokaci."

Mr. Chen Haixian ya kuma nuna damuwa kan batun sallamar ma'aikata. Bayan da ya yi nazari kan wannan batu sau da dama, ya tsaida kudurin cewa ba zai sallami ma'aikata ba. Chen Haixian ya ce, "Idan an sallami ma'aikata, mai yiyuwa ne za a samu sakamakon da ake bukata cikin dan lokaci, amma dukkan ma'aikata za su nuna damuwa, kuma ba za su iya kwantar da hankalinsu kan aiki ba, har ma za su dinga yin bacin rai. Sabo da haka, mun tsai da kudurin cewa ba za mu sallami ma'aikata ba."

Bayan da ma'aikata suka ji wannan kuduri, sun kwantar da hankalinsu kan aiki. Kuma sun soma yin kokarin taimakawa kamfanin wajen tsimin kudi domin fama da rikicin da ake fuskanta tare. Yanzu kamfanin ya soma ficewa daga mawuyacin hali. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China