A cikin bayanin, an ce, dangantakar da ke tsakanin Sin da kasashen Afirka nada karfi sosai. Dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare da ke tsakanin Sin da kasashen Afirka wanda ci gaba da kara amincewa da juna a fannin siyasa da yin hadin gwiwa a fannin tattalin arziki da koyi da juna a fannin al'adu ya dace da moriyar Sin da kasashen Afirka.
Tun daga ran 5 zuwa 14 ga wata, Yang Jiechi yana yin ziyara a kasashe 5 na Afirka da kasar Saudiyya da kasar Maldives. A cikin bayanin, ya jaddada cewa, yin hadin gwiwa tare da kasashe masu tasowa da ke hade da kasashen Afirka shi ne manufofin kasar dangane da harkokin waje.
A cikin bayanin, an ce, a cikin 'yan shekaru da suka wuce, dangantakar da ke tsakanin Sin da kasashen Afirka ta samu bunkasuwa sosai, musamman ma a cikin yanayin matsalar kudi ta duniya, hadin gwiwa da ke tsakanin Sin da kasashen Afirka ya zaman muhimmin aiki na duniya.(Abubakar)