in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana karfafa hadin gwiwar sana'o'in noma da su a tsakanin gabobi 2 na mashigin tekun Taiwan
2010-01-08 22:08:29 cri
Tun daga shekaru 80 na karnin da ya gabata, hadin gwiwar da aka yi a tsakanin gabobi 2 na mashigin tekun Taiwan a fannonin aikin gona da sana'ar su, wato sana'ar kamun kifi ta samu karfafuwa sosai, kuma ta riga ta zama daya daga cikin muhimman fannonin da ake yin mu'ammala da hadin gwiwa tsakaninsu. A yayin taron da aka yi a birnin Ningbo, wato birnin da ke bakin teku, kuma ke gabashin kasar Sin game da wannan batu, yaya za a karfafa irin wannan hadin gwiwa a yanayin da ake ciki, musamman lokacin da bangarorin biyu na mashigin tekun Taiwan suke kokarin fama da illar da aka yi musu sakamakon rikicin hada-hadar kudi na duniya ya zama muhimmin batun da ke jawo hankalin wadanda suka halarci wannan taro.

A yayin taron, Mr. Jia Qinglin, shugaban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa na kasar Sin ya bayyana cewa, jama'ar yankunan biyu da ke zaune a tsakanin gabobin biyu na mashigin tekun Taiwan za su iya samun moriya sakamakon irin wannan hadin gwiwar da ake yi a fannonin aikin gona da sana'ar kamun kifi. Mr. Jia ya ce, "Bangarorin biyu da ke tsakanin gabobi biyu na mashigin tekun Taiwan suna taka rawarsu ta musamman wajen kara yin mu'ammala da hadin gwiwa a fannonin aikin gona da sana'ar su a tsakaninsu. Tabbas ne za a samu moriya wajen sake yin amfani da karfin kawo arziki a tsakaninsu kamar yadda kamata. Haka kuma, karfin kawo arzikin aikin gona da sana'ar kamun kifi da karfin yin takara a kasuwannin duniya za su samu karfafuwa. A waje daya, wannan zai kawo fatan alheri ga manoma da masunta na bangarorin biyu."

Babban yankin kasar Sin yana kan gaba da yankin Taiwan wajen aikin gona da yawan 'yan kwadago da kuma masu kasuwanci, a waje daya, yankin Taiwan yana kan gaba da babban yanki a fannonin jari da kimiyya da fasaha da kuma hanyoyin daidaita harkokin tattalin arziki. Alal misali, yankin Taiwan yana da fasahohin zamani da dimbin ire-iren dabbobin ruwa a fannin kiwon dabbobin ruwa. A waje daya, babban yankin kasar Sin yana da kyawawan sharudan halittu na kiwon dabbobin ruwa da tasoshin ruwa da yawa da dimbin manyan filayen noman kayayyakin teku.

Kamfanin aikin gona na nishadin masu yawon shakatawa da ke birnin Quzhou na lardin Zhejiang kamfani ne da wani dan yankin Taiwan suka zuba jari suka kafa a babban yankin kasar, kuma ke cinikin furanni masu daraja da 'ya'yan itatuwa da kayan lambu na Taiwan. Ko da yake bai dade da kafuwa ba, amma yanzu ya riga ya zama wata cibiyar cinikin furanni masu daraja da gama wata cibiyar horaswa wajen noman furanni da suka shahara a tsakanin wadanda ke sha'awar furanni. Mr. Bai Guijin, shugaban kamfanin ya ce, dalilin da ya sa ya zuba jari a babban yankin shi ne ana da babbar kasuwa da isassun 'yan kwadago a babban yankin. Mr. Bai ya ce, "Yanayin wannan wuri yana da kyau. Alal misali, ana da kyawawan gonaki da isassun 'yan kwadago, kuma wannan wuri yana gabashin kasar Sin, inda ake da wata babbar kasuwa. Yankin Quzhou yana wurin da ke hada da yanayin zafi da yanayin maras zafi. Sabo da haka, ana da damar zabar furanni iri iri da ake son nomawa. Bugu da kari kuma, gonakin wannan wuri suna da inganci, kuma suna dacewa da furannin da muke nomawa."

Amma bangarorin biyu da ke tsakanin gabobin mashigin tekun Taiwan sun gamu da sabbin matsaloli a sakamakon rikicin kudi na duniya da ya auku a karshen shekarar 2008. Mr. Cheng Guoqiang wanda ke nazarin yadda za a kara yin hadin gwiwa a tsakanin babban yanki da yankin Taiwan na kasar Sin ya ba da shawara cewa, ya kamata bangarorin biyu su kara yin hadin gwiwa a fannonin kafa tsare-tsare da yin mu'sayar shawarwarin aikin gona. Mr. Cheng ya bayyana cewa, "Ya kamata bangarorin biyu su kafa tsarin yin tattaunawa kan aikin gona lokaci zuwa lokaci, kuma ci gaba da sa kaimi ga ma'aikatan aikin gona da su kai wa juna ziyara da kuma yin musayar bayanan aikin gona da kuma kafa tsarin yin hadin gwiwa kan yadda za a cinikin amfanin gona a tsakanin babban yanki da yankin Taiwan na kasar Sin. Haka kuma, ya kamata a yi kokarin kafa tsarin yin hadin gwiwa a fannin raya fasahohin zamani na aikin gona da kuma more irin wannan fasahohin zamani."

Bugu da kari, game da batun yin hadin gwiwa a sana'ar kamun kifi, Mr. Huang Yicheng, mataimakin shugaban kamfanin sana'ar kamun kifi na Huawei na yankin Taiwan ya ba da shawara cewa, "Ina fatan za a iya kafa wata unguwa a babban yankin, inda masunta na Taiwan za su iya raya sana'ar kamun kifi. Sannan za a iya kafa cibiyoyin nune-nunen kayayyakin ruwa da kifaye na Taiwan a babban yankin. Haka kuma, bangarorin biyu su iya yin hadin gwiwa wajen neman kamun karin kifaye domin raya kasuwannin kayayyakin ruwa a babban yankin, har ma a duk fadin duniya."

Game da shawarar kan yadda za a kara yin hadin gwiwa a fannonin aikin gona da sana'ar kamun kifi da bangarorin babban yanki da yankin Taiwan suka bayar cikin hadin gwiwa, Mr. Wang Yi, shugaban ofishin kula da harkokin Taiwan na gwamnatin kasar Sin ya nuna yabo sosai, inda ya ce, "Wannan shawara ta habaka fannonin yin hadin gwiwa da bangarorin biyu suke yi, kuma tana dacewa da bukatun da jama'ar bangarorin biyu suke da su. Wannan fata ne na manoma da masunta na babban yanki da na Taiwan na kasar Sin." (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China