in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashe 192 da kungiyoyin kasa da kasa fiye da 50 za su halarci bikin baje koli na duniya na Shanghai
2010-01-07 19:03:10 cri

Kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin Jiang Yu ta fayyace a ran 7 ga wata a nan birnin Beijing cewa, ya zuwa yanzu, kasashe 192 da kungiyoyin kasa da kasa fiye da 50 sun tabbatar da aniyar halartar bikin baje koli na duniya na Shanghai.

A game da labarin da jaridar Yomiuri Shimbun ta kasar Japan ta bayar kan halartar bikin baje koli na duniya na Shanghai da firaministan Japan Yukio Hatoyama zai yi da kuma ziyararsa a birnin Nanjing, Jiang Yu ta jaddada cewa, dole ne shugabannin kasashen Sin da Japan su kara zagewa wajen tuntubar juna, amma ba a iya tabbatar da wannan labari ba.

Za a yi bikin baje koli na duniya na Shanghai daga ran 1 ga watan Mayu zuwa ran 31 ga watan Oktoba na shekarar 2010, babban jigon bikin shi ne "birni ya kyautata zaman rayuwar mazauna". Yanzu, ana yin ayyukan share fagen bikin baje koli na duniya a fanin gina dakunan nune-nune da sauransu.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China