in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bayanin musamman domin murnar rana ta farko ta shekarar 2010
2010-01-02 18:29:41 cri
To, jama'a masu karanta, yau rana ce ta farko ta shekarar 2010. Barka da sabuwar shekara! Ko kuna murnar wannan rana tare da iyalai a yanzu? A duk fadin duniya, kasashe da dama suna daukar wannan rana a matsayin wata muhimmiyar ranar biki. Amma kuma sabo da matsayi na wadannan kasashe na daban-daban a duniya, shi ya sa lokacin zuwan sabuwar shekara na daban daban. Kamar kasar Tanga dake nahiyar Oceaniya ta fi wuri wajen maraba da zuwan sabuwar shekara. Amma kasar Samoa ta yamma ta fi makara wajen marabtar zuwan sabuwar shekara a duniya.

A kasar Sin, mutane su kan taya murnar zuwan rana ta farko a kowace shekara. Sun samu lokacin hutu sun je yawon shakatawa ko kuma cin abinci tare da iyalai. Wasu kananan kabilun Sin suna da al'adun kansu. Kamar kabilar Zhuang, ta kan gudanar da gasar wasanni, yayin da kabilar Dong ta kan dafa kifaye ta hanyoyi daban daban. Ban da kasar Sin, sauran kasashen duniya da dama su kan taya murnar rana ta farko ta sabuwar shekara. Bari mu ga yadda su kan yi a wannan rana.

Mutanen kasar Japan suna dora muhimmanci sosai kan zuwan sabuwar shekara. Su kan huta daga ranar 29 ga watan Disamba zuwa ranar 3 ga watan Janairu na sabuwar shekara. Su kan kira ranar 31 ga watan Disamba na kowace shekara ranar Dahui, wato ranar karshe ta kowace shekara. A wannan rana da dare, mutanen Japan su kan yi addu'a domin maraba da zuwan kyakkyawar sabuwar shekara. A wannan rana da daddare kuma, a kan kada kararrawa har sau 108 domin kau da dodanni. Mutanen Japan su kan saurari wadannan kararrawa daga baya su yi barci. Kuma ranar farko ta sabuwar shekara, a kan kira ta ranar Zheng. A wanna rana, matasa da yara su kan gai da mahaifa da tsofaffi domin nuna girmamawa. Sai su kan bakunci gidan abokai.

To, a kasar Singapore kuma, mutane su kan tashi da sassafe su gai da iyalai. Kuma su kan samu goro daga tsofaffi. Kungiyoyin nuna fasahohi su kan gabatar da shirye-shirye a kan tituna. Dukkan mutanen kasar, maza da mata, tsoffi da yara su kan yi ado su bakunci gidajen dangogi da abokai.

A kasar Birtaniya, mutane su kan kai ziyara a gidajen abokai tare da waina da giya. Ba su kada kofa ba, su kan shiga ciki kai tsaye. Wannan zai kawo alheri ga mai gida. A wannan rana da dare, a kan gudanar da bukukuwan murna, inda a kan sha giya da yin raye-raye.

Bayan haka kuma, a kasar Jamus, a kan shafe mako guda ana murna. A daidai wannan lokaci, kowane iyali zai dasa wani itacen Zong da wani itacen Heng tare da furanni a gefen kofa, wadanda suka nufi da cewa, lokacin bazara yana ko ina a duniya baki daya. Kafin zuwan sabuwar shekara, mutane su kan hau da wani kujera. Yayin da sabuwar shekara ta isa, sai su kan yi tsalle daga kujera, tare da jefa wani abu mai nauyi. Wannan ya yi nuni da cewa, za a kau da masifu a sabuwa shekara. Bayan haka, a lokacin murna, mata su kan yi wasan kwaikwayo, yayin da maza su kan shiga gasar hawan itace.

Mutanen Brazil su kan hau manyan tsanuka domin neman goron Jinhua, wanda zai kawo musu alheri. Kuma ba za a samu shi ba, sai da jaruntaka sosai.

Kasar Faransa ta kan taya murna ta hanyar shan giya daga karshen ranar tsohuwar shekara har zuwa ranar 3 ga watan Janairu ta sabuwa shekara.

Kuma a kasar Greece, kowane iyali ya kan samar da wata babbar waina, kuma ya ajiye wata kwandala a ciki. Daga baya, za a raba wannan waina ga membobin iyalin da abokai. Duk kowane ya ci rabonsa tare da kwandala, zai taka sa'a a sabuwar shekara. Kowa da kowa zai taya shi murna.

A kasar Roumania kuma, kafin zuwan sabuwar shekara, mutane su kan kafa wani itacen Christmas da dandalin shirye-shirye a filin square. Sai da dare, mutane su kan yi kide-kide da wake-wake da raye-raye domin murna.

A rana ta farko ta sabuwar shekara, mutanen Pakistan su kan fita waje tare da kayan kwalliya irin na dusa mai launin ja. Idan suka gamu da dangogi ko abokai, su kan sa shi a fuskokinsu domin kawo alheri.

A yankin arewacin Afghanistan, mutane su kan gudanar da gasar kwace awaki domin murna.

Kuma mutanen kasar Argentina suna tsammani cewa, ruwa ya fi tsarki a duniya. A sabili da haka, mutanen su kan yi wanka a kogi domin kau da dauda.

A wasu yankunan kasar Mecixo, an hana yin murmushi a yayin zuwan sabuwar shekara. A kasar kuma, an raba shekara daya zuwa watanni 18, kuma kowane wata yana kunshe da kwanaki 20. An hana yin murmushi a karshen kwanaki biyar na kowace shekara.

A kasar Bulgaria, a yayin cin abinci a ranar farko ta sabuwar shekara, wanda ya yi atishawa zai kawo alheri ga iyalai, sai mai gida zai ba shi kyautar doki ko sauransu.

A kasar Tanzaniya kuma, kafin zuwan sabuwar shekara, 'yan kabilar Swahili su kan zuba masara a ko ina a gidajensu, da nufin kau da dodanni da neman samun alheri. Kuma su kan ajiye abinci mai dadi a gaban kofa, masu tafiye-tafiye za su iya cin wadannan abinci da kansu. A ranar sabuwar shekara, mutane su kan yi wanka a ruwan teku domin kau da dauda.

To, jama'a masu karanta, a cikin shirinmu na yau, mun gabatar muku da al'adu irin daban daban na kasa da kasa a yayin murnar ranar farko ta sabuwar shekara. Da fatan zai nishadantar da ku. (Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China