in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wasu 'yan diplomasiyya sun kai ziyara ga masana'antun kasar Sin
2009-12-31 16:26:04 cri
A kwanan baya, babbar hukumar sa ido kan ingancin kayayyaki ta kasar Sin ta gayyaci jami'an diplomasiyya na kasashe fiye da 20, ciki har da na kasashen Amurka, Rasha da Masar da suke nan kasar Sin sun kai ziyara ga hukumomin dudduba da sa ido kan ingancin kayayyaki da wasu kamfanonin sarrafa abinci da masana'antun yin tufafi da na kera motoci da ke lardunan Jiangsu da Zhejiang da birnin Shanghai da suke gabashin kasar Sin domin samun masana kan yadda kasar Sin ke sa ido kan ingancin kayayyaki kai tsaye.

Kamfanin Youngor da ya shahara sosai wajen samar da tufafi irin na salon yammacin duniya na daya daga cikin muhimman kamfanoni da masana'antun da jami'an diplomasiyya na kasashen waje da ke nan kasar Sin suka kai ziyara. Tun daga karshen shekara ta 2008, rikicin hada-hadar kudi ya auku a duk fadin duniya. Ko shakka babu, wannan rikici ya kawo illa ga kamfanin Youngor. Amma ya kasance tamkar wani babban kamfanin da ke da ma'aikata fiye da dubu 50, lokacin da yake kokarin tinkarar wannan rikici a kasuwannin kasashen waje, yana kuma kokarin neman damar sayar da karin tufafi a kasuwannin cikin gida. A shekarar 2009, yawan tufafin da kamfanin Youngor ya sayar a kasuwannin kasashen waje ya ragu da kashi 5 cikin dari, amma a waje daya, yawan tufafin da ya sayar a kasuwannin cikin gida na kasar Sin ya karu fiye da kashi 20 cikin dari. Mr. Li Rugang, mataimakin shugaban kamfanin Youngor ya bayyana cewa, "Bisa shirin da kamfaninmu ya tsara, muna sayar da tufafin da yawansu ya kai kashi 50 cikin dari a kasuwannin cikin gida, a waje daya, muna sayar da sauran kashi 50 cikin dari a kasuwannin kasashen waje. Alal misali, yawan tufafin da muka dinka ya kai miliyan 2 a shekara daya, muna sayar da tufafi miliyan daya daga cikinsu a kasuwar cikin gida, a waje daya, muna sayar da sauran tufafi miliyan 1 a kasuwannin ketare. A shekarar da muke ciki, yawan tufafin da muka sayar a kasuwar cikin gida ya karu da kashi 20 cikin dari bisa na shekarar 2008, amma yawan tufafin da muka sayar a kasuwannin ketare ya ragu da kashi 5 cikin dari bisa na shekarar 2008. A shekarar 2008, jimillar kudaden da muka samu domin sayar da tufafi ta kai kudin Sin yuan biliyan 21.4, amma a shekarar 2009, wannan adadi zai kai biliyan 24, wato za ta karu da kashi 15 cikin dari."

Tufafi masu inganci su ne suke goyon bayan kamfanin Youngor. Tun daga shekarar 1979, kamfanin Youngor, wato wani karamin kamfani ne a wancan lokaci ya soma samar da tufafi irin na salon yammacin duniya. Bayan da ta yi kokari cikin shekaru 30 da suka gabata, kamfanin yana da tamburan tufafi guda 6 da suka shahara a kasar Sin, har a kasuwannin duniya. Daga cikinsu, tambarin tufafin salon yammacin duniya yana kan gaba a kasuwar kasar Sin a cikin wasu shekarun da suka gabata. Mr. Li Rugang, ya kara da cewa, dalilin da ya sa kamfanin yake samun ci gaba kamar haka shi ne kamfanin yana mai da hankali kan ingancin kayayyaki ba tare da kasala ba.

"Muna mai da hankali sosai kan inganci da tambari na kayayyakinmu a kullum. A lokacin da ake cikin shekaru 80 na karnin da ya gabata, mun soma kafa tambari, da kuma sa ido kan ingancin kayayyaki. A kowace ajandar yin tufafi, muna da ma'aikacin da ke sa ido kan kayayyaki, kuma muna sa ido kan inganci har sau biyu ko sau uku."

Lardin Zhejiang da kamfanin Youngor yake ciki muhimmin sansani ne da ke samar da kayayyakin saka tufafi da takalma a nan kasar Sin. Ana sayar da kayayyakinsu a kasuwannin kasashen Turai da Amurka da kuma a kasashen Afirka. Amma lokacin da yawan kayayyaki kirar kasar Sin da ake sayarwa a kasuwannin ketare ke ta karuwa, kasashen yammacin duniya su kan dauki matakan kayyade shigar da kayayyaki kirar kasar Sin. Sakamakon haka, masana'antun kasar Sin da yawa sun samu illa sosai.

Game da ingancin kayayyaki kirar kasar Sin, Mr. Alberto Alonso Diaz, jami'in kula da harkokin kasuwanci a ofishin jakadancin kasar Spaniya da ke nan kasar Sin, ya gaya wa wakilinmu cewa, bayan da ya yi wannan rangadi a masana'antu da kamfanonin kasar Sin, yana ganin cewa, ingancin kayayyaki kirar kasar Sin yana dacewa da ma'aunin kungiyar EU da bukatar da kungiyar take da ita. Kasar Spaniya za ta ci gaba da shigar da kayayyaki kirar kasar Sin. Mr. Alberto Diaz ya ce, "Kamar yadda ka sani, kasar Spaniya ta shigar da kayayyakin saka da takalma da kayayyakin wasa na yara da yawa daga kasar Sin. Yanzu, kungiyar EU ta dauki matakin sa takunkumi kan takalma kirar kasar Sin. Amma kasarmu za ta kyale irin wannan matakin da aka dauka, kuma za ta ci gaba da shigar da dimbin takalma kirar kasar Sin. Game da wannan ziyara, a ganina, kayayyaki kirar kasar Sin suna da kyau, suna dacewa da ma'aunin da kungiyar EU ta tsara. Haka kuma na ga hukumomin sa ido kan ingancin kayayyaki na matakai daban daban na sa ido kan ingancin kayayyaki kamar yadda ya kamata."

Kamfanin Haitong mai sarrafa abinci kamfani ne da ke sarrafa kayayyakin lambu da 'ya'yan ituwa, kuma yana fitar da kayayyakinsa zuwa kasashen Japan da Amurka. Ya kasance tamkar wani muhimmin kamfanin sarrafa amfanin gona a kasar Sin, kamfanin Haitong yana sarrafa amfanin gona bisa ma'aunonin da aka tsara domin kasuwannin kasashen duniya. Mr. Sun Jincai, babban daraktan kamfanin Haitong mai sarrafa abinci ya bayyana cewa, "Muna da wani ofishin tabbatar da ingancin abinci a kamfaninmu. Mun shigar da tunanin sa ido kan ingancin abinci daga gonaki har zuwa teburin cin abinci, wato mun soma sa ido kan yadda ake yin shuke-shuke da sarrafa amfanin gona da zirga-zirgarsu da kuma ta sayar da abinci. Sakamakon haka, muna sa ido kan ingancin abinci daga farko har zuwa karshe."

A cikin 'yan shekarun da suka gabata, bi da bi ne gwamnatin kasar Sin ta dauki matakai iri daban daban wajen sa ido da kuma kyautata ingancin abinci. Mr. Wei Chuanzhong, mataimakin shugaban babbar hukumar sa ido kan ingancin kayayyaki ta kasar Sin ya ce, "Mun kuma kafa tsarin tabbatar da ingancin abincin da ake shige da fice, kuma muna kyautata tsarin dudduba ingancin kayayyaki da ingancin abinci a kai a kai. A cikin shekaru da yawa da suka gabata, galibin abincin da kasar Sin take fitarwa yana biyan bukatar da ake da ita a kasuwannin kasashen yammacin duniya."

Kasar Amurka na daya daga cikin muhimman kasashen da suke shigar da kayayyaki kirar kasar Sin. Bayan da ya yi rangadin aiki a kamfanonin sarrafa abinci da hukumomin sa ido kan ingancin kayayyaki na kasar Sin, Mr. William Westman, ministan ofishin jakadancin kasar Amurka da ke nan kasar Sin ya bayyana cewa, ya kamata bangarorin sa ido kan ingancin kayayyaki na kasashen Amurka da Sin su amince da juna.

"Abin da yake da muhimmanci shi ne ya kamata bangarori biyu su amince da takardun tabbatar da ingancin abinci da hukumomin sa ido kan kayayyaki na kasashen biyu suka gabatarwa juna. Ko da yake har yanzu ba a kulla wata irin wannan yarjejeniya ba tukuna, amma aminci yana kasancewa a tsakaninmu. Ya kamata bangarorinmu biyu dukkanmu mu amince da takardun tabbatar da ingancin kayayyaki da bangarorinmu suka gabatarwa juna."

Kamfanin kera na'urorin wanke tufafi na Little Swan na birnin Wuxi da ke lardin Jiangsu na daya daga cikin kamfanonin da 'yan diplomasiyya suka kai ziyara. Lokacin da suke tsayawa a gefen layin kera na'urorin wanke tufafi na wannan kamfani, Mr. Mono Mashaba, jami'i mai kula da harkokin aikin gona a ofishin jakadancin kasar Afirka ta kudu da ke nan kasar Sin ya ce, yanzu ya yi imani sosai ga ingancin kayayyaki kirar kasar Sin. Ya ce, "Na gode wa bangaren kasar Sin da ya gayyaci 'yan diflomasiyya da su kai ziyara ga kamfanonin da suke fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje. Ina tsammanin cewa, wannan ziyara tana da muhimmanci sosai. Yanzu mun san yadda masana'antu da kamfanoni na kasar Sin suke kera da kuma samar da kayayyaki, kuma yadda hukumomin gwamnatin kasar Sin suke sa ido kan ingancin kayayyaki. Sakamakon haka, mun yi imani sosai bisa ga kayayyaki kirar kasar Sin." (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China