in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bayani kan tsohon shugaban kasar Sin marigayi Mao Zedong mai girma
2009-12-28 15:34:11 cri
To, jama'a masu karanta, kwanan biyu ba mu gamu da juna ba, yaya jiki? Yaya aiki? A makon jiya, mun samu sakwanni da dama daga wajenku, wadanda suka kara kwarin gwiwarmu kwarai da gaske. Yanzu bari mu karanta wasu daga cikinsu. Malam Salisu Muhammed Dawanau daga Abuja, tarayyar Nijeriya, ya rubuto mana cewa, "A makonni biyu da suka shude, na yi tafiye-tafiye sosai. A makon jiya kuma mun tafi Minna, jihar Neja, don halartar wani kwas da ofishinmu ya gudanar. A gaskiya, rashin zamana a ofis ne ya haifar da ba ku samu wasika daga gare ni ba. Sai dai yanzu Allah Ya dawo da ni lafiya. Kuma ko a can inda na tafi, ina sauraronku a kullum sabo da ina tare da rediyona. Kun san an ce 'tafiya mabudin ilmi', wadannan tafiye-tafiye da na yi sun dada mini ilimi game da yadda wasu mutane su kan yi rayuwarsu na yau da kullum. A Birnin Minna kuma na hadu da wasu Sinawa a wani wurin cin abinci na MR. BIGG'S. Mun gai da su har mun yi hira. Sinawan suna aiki ne da wani kamfanin kasar Sin mai suna 'CCECC'. Da fatan ayyuka suna tafiya daidai-wa-daida kamar yadda kuke bukata."

To, mun gode ainun da saduwa da wasikarka, malam salisu a Abuja, tarayyar Nijeriya. A bakin Sinawa akwai wani karin magana cewa, "Du wan juan shu, xing wan li lu", wanda ya nufin cewa, kamata ya yi a karanta littattafai sama da dubu 10, tare da yin tafiye-tafiya sama da kilomita dubu 5 a cikin zaman rayuwa. Sabo da littattafai za su kara ilmi, yayin da tafiye-tafiye za su bude idanu. Mutane za su ci moriya daga su biyu tare. A sabili da haka, yanzu mutanen kasar Sin da dama suna aiki ko kuma dalibta a ketare domin kara ilmi da bude idonsu. Muna fatan dukkansu suna cikin koshin lafiya tare da samun babban ci gaba. Amin!

To, sakon malam Salisu ke nan. Bayan haka, malam mai tsako Abdoulaye Djibrila daga Kribi a jamhuriyar kamaru ya aiko mana da wasika cewa, "Zan ba ku wata shawara kan shirye-shiryenku. Ra'ayina shi ne, ku dinga tura ma'aikatan sashen hausa na gidan radiyon Sin, sinawa kamar su Bello wang da Bilkisu da sauransu zuwa nahiyar Afrika, kamar Nijeria da Nijer a gidajen yada labarun na sashen hausa, su yi ko watanni uku-uku a nahiyarmu Afrika."

To, mun gode, malam mai tsako Abdoulaye Djibrila. A hakika dai, nan ba da dadewa ba, ma'aikatanmu biyu za su je Nijeriya, wato Danladi zai je tashar 'yan jarida ta CRI a Nijeriya domin aiki, yayin da Musa zai samu karatu a can. Shi ya sa ba za mu samu isassun ma'aikata wajen aiki ba. Duk da haka kuwa, za mu yi la'akari kan shawarar da ka bayar da kokarta samar da kyawawan shirye-shirye, da fatan za ka ci gaba da mai da hankali kan tasharmu ta CRI da ba da shawarwari masu kayu. Allah ya karfafa dankon zumunci a tsakaninmu.

To, bayan haka, kwanan baya, malam Ali Buge Kiragi ya rubuto mana wani sako ta yanar gizo ta internet, inda ya bayyana cewa, "Don Allah ku ba ni tarihin madugun gina kasar Sin marigayi malam Mao Zedeng, ina dalilin da ya sa ana cewa ya rasu amma har yanzu Sinawa suke tunawa da shi?" Yanzu za mu kokarta amsa wannan tambaya.

An haifi Mao Zedong a ran 26 ga watan Disamba na shekarar 1893 a wani iyalin manoma. Daga shekarar 1914 zuwa shekarar 1918, ya samu karatu a kwalejin horar da malamai na farko na lardin Hunan. Daga bisani, a shekarar 1920, ya kafa kungiyar gurguzu a lardin Hunan.

A watan Yuli na shekarar 1921, Mao Zedong ya halarci taro a karo na farko na wakilan Sin bayan kafuwar jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin. Daga baya, a shekarar 1923, ya halarci taron a karo na biyu, inda aka mayar da shi a matsayin wakilin gudanarwa na kwamitin tsakiyar JKS. A shekarar 1924 bayan hada gwiwa tsakanin JKS da jam'iyyar Kuomintang, ya zama karin wakilin gudanarwa na kwamitin tsakiya, kuma ya tsara jaridar siyasa a kowane mako. A watan Nuwamba na shekarar 1926, Mao Zedong ya zama darektan kwamitin kula da ayyukan manona na kwamitin tsakiya na JKS.

Daga lokacin sanyi na shekarar 1925 zuwa lokacin bazara na shekarar 1927, Mao Zetong ya gabatar da littattafai da dama, kamar "Nazari kan azuzuwan zamatakewar al'umma ta kasar Sin" da "Rahoto kan ayyukan manoma a lardin Hunan" da dai sauransu, inda ya bayyana muhimmin matsayi na batun manoma a yake-yaken Sin da muhimmancin yake-yaken manoma bisa jagorantar ma'aikata ba tare da dukiyoyi ba.

Bayan da jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da jam'iyyar Kuomintang suka bata, a gun taron gaggawa na kwamitin tsakiya na JKS da aka yi a watan Agusta na shekarar 1927, Mao Zedong ya bayyana ra'ayinsa na samun mulki ta hanyar yin yake-yake. Sai a watan Oktoba na shekarar 1934, sojojin JKS sun fata yin dogon tafiye-tafiye. A watan Janairu na shekarar 1935, hukumar siyasa ta kwamitin tsakiya ta gudanar da taron Zunyi, inda ta dauki malam Mao a matsayin shugaban kwamitin tsakiya. Daga bisani, a watan Oktoba na shekarar 1935, an kammala wadannan dogon tafiye-tafiye a arewacin lardin Shannxi.

Bayan yakin hare-hare da sojojin Japan suka yiwa kasar Sin na tsawon shekaru 8 da yakin basusu na tsawon shekaru 3, a ran daya ga watan Oktoba na shekarar 1949, an kafa jamhuriyyar jama'ar Sin. Kuma Mao Zedong ya zama shugaban gwamnatin tsakiya ta jama'a. A shekarar 1954, taro a karo na farko na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ya zartas da tsarin mulki na jamhuriyyar jama'ar Sin da Mao Zedong ya tsara. Dadin dadawa, Mao Zedong ya hau kujerar shugaba na farko na jamhuriyyar jama'ar kasar Sin.

A ran 9 ga watan Satumba na shekarar 1976, malam Mao Zedong mai girma ya rasu a birnin Beijing. A cikin duk rayuwarsa na tsawon shekaru 83 a duniya, ya saddaukar da kansa ga yake-yaken jama'a, kuma ya ceci jama'ar Sin dubu-dubai daga duhun kai da wahalhalu masu tsanani. A sabili da haka, mutane su kan ce, marigayi Mao Zedong mai girma yana rayuwa a zukatansu har abada.

To, bayani ke nan kan tambayar malam Ali, da fatan ka ji ka gamsu da shi. Bayan haka, a makon jiya, mun samu sakwanni da dama daga wajen masu sauraronmu, ciki har da wani daga malam Abba Tahir daga tarayyar Nijeriya ta yanar gizo ta internet, da malam Sani Muhammed, daga Bauchi, tarayyar Nijeriya da dai sauransu, wadanda ba mu iya karanta sakwanninsu duka ba, sabo da karancin lokaci. Don haka muna farin ciki, da fatan za ku ci gaba da mai da hankali kan shirye-shiryenmu. (Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China