in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Birnin Beijing ya samu babbar sauyawa a cikin 'yan shekaru 30 da suka gabata
2009-12-14 20:48:20 cri
Masu karatu, muna fatan kuna cikin koshin lafiya. A cikin shirinmu na yau, mun gayyaci masana uku a fannin harshen Tamil, wadanda suka zo daga Indiya da Sri Lanka da dai sauransu. Kuma sun yi aiki a sashen Tamil na gidan rediyon CRI a cikin 'yan shekaru 40 da suka gabata. Za su waiwaya baya su gaya mana cewa, yaya zaman rayuwarsu a kasar Sin a wancan lokaci.

Malam Kadikaa Chalam, yana daya daga cikin masanan da suka fi dadewa suna aiki a sashen Tamil na CRI. A shekarar 1983, ya zo kasar Sin a karo na farko. Bayan shekaru 21 kuma, wato a shekarar 2004, ya koma gida. Ya shafe shekaru kimanin 20 yana nan kasar Sin, a sabili da haka, ya ga babbar sauyawar birnin Beijing na Sin a kai a kai. Ya yi alfahari da cewa, ya gani sauyawar kasar Sin da ta fi bude kofa ga kasashen waje. Kuma kimiyya da fasaha na zamani da fasahohin samun bunkasuwa sun shiga kasar Sin daga ketare. A farkon lokacin gudanar da manufar bude kofa ga kasashen waje da yin kwaskwarima a gida, ana karancin kayayyaki sosai. ba za a sayi kome ba sai da tikitoci iri iri. Bayan shekaru 10 kawai, akwai kowane abin da aka bukata a kantuna a Sin, har ma da wasu kayayyakin da aka shigo da su daga ketare. A shekarar 1999, Kadikaa Chalam ya kawo ziyara a Sin a karo na 3, a lokacin,an canja fuskar wasu birane. An kafa gine-gine masu hawa da yawa da hanyoyi masu fadi sosai a can. Kuma albashinsa ya karu daga kudin Sin yuan daruruka zuwa kimanin dubu 10 a kowane wata. Ya bayyana wa wakilinmu cewa,

"A farkon shekaru 80 na karnin da ya gabata, Sin ta fara bude kofa ga kasashen ketare. Na iya tunani sosai da matsalolin da karancin kayayyakin masarufi na yau da kullum ya haddasa. Bayan da muka fara rayuwa a sabon dakinmu a birnin Beijing, ba mu iya samun kyawawan labule ba. Kuma zane ba mu samu cikin sauki ba. Ba a sayi kayayyakin masarufi ba sai an je kantin Youyi mai nisa sosai tare da tikiti. Bugu da kari, mun yi takatsantsan da garin. Im ba haka ba, ba mu iya samun isashen abinci a karshen wata ba. A sakamakon haka, tikitin ya burge ni sosai."

A shekarar 2003, malam Raajaaram daga gidan rediyon Indiya ya fara zaman rayuwarsa a kasar Sin tare da gargadin da abokansa suka yi masa. Amma a kai a kai ya fara fahimtar kasar Sin. Bayan da Sin ta bude kofa ga kasashen waje, ba ma kawai kimiyya da fasaha na kasashen yammacin duniya suka zo ba, hatta ma sabuwar hanyar rayuwa, wadda ta canza rayuwar matasa sosai. malam Raajaaram ya furta cewa, ra'ayin Sinawa na bude kofa ya aza tubalin raya huldar diplomasiyya tsakaninta da sauran kasashen duniya. Ga abin da ya ce,

"Yayin da na iso kasar Sin, wata sabuwar gwamnatin kasar ta fara aiki. Kuma jiragen kasa sun kara sauri. Na je Shaolinsi da birnin Shenzhen tare da abokan aikina ta jirgin kasa, awoyi 10 ne kawai sai na isa. Na fahimci 'saurin kasar Sin' dake kara karuwa. Bayan haka, wasu kamfanonin ketare sun zo kasar Sin, yayin da wasu kamfanonin Sin suka je ketare. A kasar Indiya, kayayyakin Sin sun yi suna sosai."

Idan aka kwatanta da malam Chalam da malam Raajaaram, ba shakka, Maria Michael da matarsa Mary Fraskal dake rayuwa a birnin Beijing sun taka sa'a. Suna jin dadin zaman duniya, kuma suna iya kai ziyara a filin wasan motsa jiki na kasar Sin mai sifar shekar tsuntsu da babban dakin wasan kwaikwayon kasa da babban titi mai suna Qianmen domin kara fahimtar birnin Beijing mai dogon tarihi.

A cikin waka mai dadin ji, Maria Michael da matarsa sun fara rayuwa a wannan rana. A cikin 'yan shekaru 2 da suka gaba a birnin Beijing, sun riga sun saba da abincin Sin domin kiwon lafiya. Kuma sun fara motsa jiki tare da makwabtansu. Suna kokarin sabawa da zaman rayuwa a wannan birni.

Bayan kammala aiki, Maria da matarsa sun fi sha'awar yawon shakatawa. Su kan yi bulaguro a birnin Beijing, daga babban titin Wangfujing zuwa tsoffin hanyoyi da ake kira Hutong, daga Babbar Ganuwa zuwa lambun shan iska dake kusa da gidansu. Daga bisani, sun kai ziyara a birnin Tianjin da Shanghai da Xi'an da Guizhou, suna jin dadi sosai ta jirgin sama. Ko da yake ba su iya magana da Sinanci ba, amma wannan ba ya kawo musu cikas ko kadan. Kuma Mary Fraskal ta nuna babban yabo ga kayayyakin kasar Sin, ta furta cewa,

"Ko a birnin Shanghai, ko a birnin Xi'an, duk lokacin da na ga kayayyaki irin daban daban, sai na saya da yawa domin ba da kyauta ga dangogi da abokai."

Mary Fraskal ta taba aiki a wata makarantar midil. A kasar Indiya, bayan aure, mata kashi 90 cikin dari ba za su ci gaba da aiki ba. Kafin shekaru 2 da suka wuce, yayin da ta zo kasar Sin tare da mijinta, ta riga ta share fagen watsi da aikinta. Amma abin mamaki shi ne, bayan da ta zo Sin, ta sami damar ba da darasi. Tun bayan shekarar 2008, ta fara aiki a kwalejin koyon harsunan waje na jami'ar koyon ilmin watsa labarai. Ta yi farin ciki kwarai da gaske.

Kamar yadda Maria Michael da matarsa suke yi, mafi yawan mutanen ketare sun fara rayuwa da aiki a Sin. Burin Sin ya jawo hankulan mutanen Indiya zuwa kasar Sin. Maria ya bayyana cewa, abokansa Moohan Bhandari da Rajeev Singh su ne haka. A cikin 'yan shekaru 3 da suka gabata ne kawai, Moohan Bhandari mai horar da Yoga daga birnin Rishikesh ya kafa wata makarantar koyon Yoga, wadda taKE kunshe da cibiyoyi 51 a duk fadin kasar Sin. Rajeev Singh mai shekaru 27 da haihuwa, wanda aka haife shi a birnin Assam, ya riga ya zama shugaban otel Tandoor a birnin Chengdu daga wani ma'aikaci a dakin abinci. Ganin mafi yawan abokai suna rayuwa a Sin yadda ya kamata, Maria Michael ya yi farin ciki, ya bayyana cewa, neman nau'in rayuwa irin daban daban ya ba da babban zarafi ga wasu mutanen Indiya masu jaruntaka sosai. Ga abin da ya ce,

"Kuzari da zarafi dake cike biranen Sin sun nuna cewa, ma'aikaci zai iya zama shugaban otel, yayin da mai ba da horo zai zama CEO. Sin tana karbar mutane daga kasa da kasa. Na yi imani cewa, yawan mutanen Indiya da za su nemi zuwan kasar Sin zai kara karuwa a nan gaba."

Bayan haka, Maria Michael ya gano cewa, a lokacin bude kofa ga kasashen waje, Sin tana canjawa a kai a kai. Kasar Sin ba ma kawai za ta karbi abubuwa daga ketare ba, har ma za ta gabatar da kyawawan al'adu ga duniya baki daya. Ya furta cewa,

"Na ji an ce, za a kafa wani kwalejin Confucius a garina Tamil Nadu. Kuma mutanen kasa da kasa suna koyon Sinanci cikin yakini. Masu nuna fasahohi na Sin suna shaidawa a kasashen ketare. Kuma gasar Olympic ta bayyana karfin kasar Sin ga duk fadin duniya. A lokacin abkuwar matsalar kudi ta duniya, Sin ta tura kungiyoyin saye-saye a ketare, domin ba da taimako, a yunkurin tinkarar matsalar kudi tare. A ganina, Sin tana kokarin canza matsayinta."

Yayin da Sin take kara shiga cikin harkokin duniya, mafi yawan mutanen ketare sun kai ziyara a can domin samun bunkasuwa. Kuma suna mai da hankali kan sauyawar kasar Sin a kai a kai.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China