in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An soma safarar man gas daga kasar Turkmenstan zuwa kasar Sin
2009-12-14 17:15:40 cri
A ran 14 ga wata a wata masana'antar sarrafa man gas ta kasar Turkmenstan, an yi bikin soma safarar man gas ta bututun da aka shimfida a tsakanin kasar Sin da kasashen Turkmenstan da Kazakhstan da Uzbekistan wadanda suke yankunan tsakiyar nahiyar Asiya. Shugaba Hu Jintao na kasar Sin wanda ke yin ziyara a kasar Turkmenstan da takwarorinsa na wadannan kasashe 3 dukkansu sun halarci wannan biki.

A yayin bikin, wadannan shugabannin kasashe 4 sun bayar da jawabai bi da bi, sannan sun bude makullin bututun tare.

Wannan bututun safarar man gas da tsawonsa ya kai kilomita 1833 ya tashi daga bakin iyakar da ke tsakanin kasashen Turkmenstan da Uzbekstan, sannan ya wuce kasashen Uzbekstan da Kazakhstan ya isa garin Holgos na kasar Sin. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China