Mr. Peres ya ce, lamarin kona masallaci, wato wani laifi mai tsanani sosai, yana sabawa da tunanin girmamawa dukkan addinai da masu bin addinai da kasar Isra'ila take bi. Haka kuma ya nemi gwamnati da rundunar sojojin tabbatar da kura da sauran hukumomin da abin ya shafa su dauki dukkan matakan da suka wajaba domin kai wadanda suka yi wannan laifi a gaban kotu.
A ran 11 ga wata da assalatu, ba tare da izini ba ne wasu Yahudawa sun kutsai kai cikin kauyen Yasuf da ke yammacin gabar kogin Jordan, kuma sun kona wani masallaci na wannan kauye. Dukkan littattafai na wannan masallaci sun kuma yi kone kumus. (Sanusi Chen)




