in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Labaru daga jaridun Afirka
2009-12-10 20:06:59 cri

A cikin shirinmu na yau, bari mu fara duba wani bayani da muka samu daga shafin internet na Garowe online na kasar Somaliya, wanda aka rubuta a ran 9 ga wata, inda shugaban kasar Somaliya ya sa kaimi ga sojojin jiragen ruwa da su yaki 'yan fashi na teku.

A ran 9 ga wata, shugaban kasar Somaliya Sheikh Sharif Sheikh Ahmed ya kai ziyara a sansanin sojojin jiragen ruwa na kasar, inda ya sa kaimi ga sojojin jiragen ruwan da su yaki da 'yan fashi na teku.

Sheikh Sharif ya ce, sojojin jiragen ruwa suna da muhimmanci kwarai da gaske wajen tsaron kasa, ya sa kaimi gare su da su hada kansu domin kare jama'a da kasarsu. Ya gaya wa sojojin jiragen ruwa a Mogadishu cewa,

'Sojoji suna matsayin masu kare kasa, sabo da haka ya kamata ku shirya sosai wajen tsaron kasa da yaki da abokan gaba, wadanda suka lalata mutuncin kasar Somaliya.'

Ahmed ya mayar da 'yan fashi na teku a matsayin wawaye ne da ke karancin kudade, ya kai suka gare su wajen lalata zaman lafiya a ruwan teku.

Amma wasu mutane sun nuna bambancin ra'ayoyinsu ga shugaban kasar Somaliya Sheikh Sharif, sun ce, dalilin da ya sa shugaban ya sa kaimi ga sojojin jiragen ruwa shi ne, domin yana son neman kudin taimako da aka ba shi, sabo da sojojin jiragen ruwa na Somaliya ba su da kwarewa wajen daidaita matsalar 'yan fashi na teku.

A 'yan kwanakin baya, shugaba Ahmed ya ki amincewa da wata yarjejeniyar kawar da bambancin ra'ayoyi, wadda gwamnatinsa ta tattauna da shugaban jihar Puntland ta kasar Somaliya Abdirahman Mohammed Farole a birnin Nairobi na kasar Kenya.

Firayin ministan Somaliya Omar Abdirashid Sharmarke da Farole sun daddale wata takarda ta wa'adi na farko ta yarjejeniyar kawar da bambancin ra'ayoyi a ran 23 ga watan Agusta a garin Galkayo da ke tsakiyar Somaliya, inda bangarorin biyu suka yarda da more albarkatun kasar.

Kamata ya yi yarjejeniyar kawar da bambancin ra'ayoyi ta taka wata muhimmiyar rawa wajen yaki da 'yan fashi na teku, wadanda suka gudanar da ayyukansu a gabar teku ta jihar Puntland.

Jama'a masu karatu, bayan haka kuma bari mu sake duba wani labari da muka samu daga cibiyar watsa labarai ta MDD, wanda aka buga a ran 9 ga wata, inda aka bayyana cewa, ko da yake an kai farmaki kan sojojin kiyaye zaman lafiya na MDD da ke a yankin Darfur na kasar Sudan, amma za su ci gaba da ayyuka cikin yakini.

A 'yan kwanakin baya, an kai farmaki sau biyu kan sojojin kiyaye zaman lafiya cikin hadin gwiwar MDD da kungiyar tarayyar Afirka wato AU a yankin Darfur na kasar Sudan, sakamakon haka sojojin kiyaye zaman lafiya 5 sun raya rayukansu, babban sakataren MDD Ban Ki-moon da sauran shugabannin kasashen duniya sun kai suka da babbar murya kan farmakin da aka kai wa sojojin kiyaye zaman lafiya.

A ran 9 ga wata, mataimakin babban sakataren MDD mista Alain LeRoy ya gaya wa manema labaru cewa, sojojin kiyaye zaman lafiya ba su jin tsoro a Darfur, kuma za su ci gaba da ayyukansu.

Mista Alain LeRoy ya jaddada cewa, a halin yanzu sojojin kiyaye zaman lafiya suna tsayawa a kan bakansu sosai domin kada a sake kai musu farmaki, amma suna mai da ayyukansu a matsayin farko, domin kare zaman lafiyar jama'a na yankin Darfur.

Malama Susana Malcorra, mataimakiyar babban sakataren MDD da ke kula da harkokin nuna goyon baya ga sojojin kiyaye zaman lafiya na kasa ta bayyana cewa, a ganinta, abun da ya fi muhimmanci shi ne, kara tabbatar da tsarin zaman lafiya na ma'aikatan MDD a yayin da suke fama da kalubaloli masu kara yawa.(Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China