in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta kyautata manufofin sayayya
2009-12-09 20:27:11 cri
Kasar Sin za ta ci gaba da kyautata wasu manufofin sayayya. Sakamakon haka, za ta iya habaka bukatun da ake da su a kasuwannin cikin gida domin tabbatar da ci gaban tattalin arzikinta cikin sauri ba tare da tangarda ba.

A ran 9 ga wata, Wen Jiabao, firayin ministan kasar Sin ya shugabanci taron aiki na zaunannun wakilan majalisar gudanarwa ta kasar, inda aka tsai da kuduri cewa, za a ci gaba da aiwatar da manufar tallafawa manoma wadanda suke sayen motoci har karshen shekara mai zuwa, kuma za ta ci gaba da tallafawa, da kuma kara tallafin kudi ga wadanda suke sayen injunan aikin gona. Sannan za ta ci gaba da samar wa jama'a na'urorin ba da haske masu tsimin wutar lantarki. Bugu da kari kuma, za ta ci gaba da aiwatar da manufar dakatar da buga harajin sayayya ga motoci masu lita 1.6 da sauran motoci masu kananan injuna har karshen shekara ta 2010. Bugu da kari kuma, idan ana son mayar da tsohuwar mota domin sayen wata sabuwar mota, gwamnatin kasar za ta samar da tallafin kudi da yawansa ya kai kudin Sin yuan dubu 5 zuwa dubu 18.

Bugu da kari kuma, gwamnatin kasar Sin za ta nuna goyon baya ga masana'antu wadanda suke cikin mawuyancin hali da su dakatar da biyan kudin inshora na ma'aikatansu, kuma za ta tallafawa irin wadannan masana'antu. A waje daya, lokacin da suka rasa aikin yi suke kokarin raya tattalin arziki da kansu, gwamnatin za ta ci gaba da rage wasu harajin da ake bugawa a cikin shekara 1 mai zuwa. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China