Wannan bayanin edita ya ce, yanzu tattalin arzikin kasar Sin yana samun farfadowa da karuwa sakamakon jarin da gwamnati ta zuba. Sabo da haka, a nan gaba dole ne a kara mai da hankali kan yadda za a habaka bukatun da jama'a suke da su domin kara bukatun da ake da su a kasuwar cikin gida. A waje daya, za a iya sa kaimi ga jama'a da su zuba jari da kansu domin kara ainihin karfin raya tattalin arzikin kasar.
Haka kuma, wannan bayanin edita ya ce, lokacin da ake tsara shirin raya tattalin arziki cikin hali mai dorewa domin karuwar tattalin arziki kamar yadda yake ciki yanzu, dole ne a kara karfin kirkiro sabbin fasahohin zamani da daidaita tsarin tattalin arziki a babban mataki. Sannan dole ne a sa kaimi wajen raya sabbin sana'o'in zamani domin tattalin arzikin kasar zai iya samun ci gaba cikin daidaito, kuma zai iya kai wani sabon mataki mai inganci. (Sanusi Chen)