A ran 5 ga watan Disamba, rana ce ta masu aikin sa kai ta duniya. A cikin 'yan kwanakin da suka gabata, kungiyoyin matasa da na masu aikin sa kai na matakai daban daban na kasar Sin sun shirya bukukuwa iri iri domin murnar wannan rana.
Wani jami'in kwamitin tsakiya na matasa masu bin kwaminisanci na kasar Sin ya bayyana cewa, bayan da kwamitin ya yi kira ga matasa da su yi aikin sa kai ga jama'a a shekarar 1993, ya zuwa yanzu, yawan mutanen da suka taba yin aikin sa kai ga jama'a ya riga ya kai fiye da miliyan 403. (Sanusi Chen)