in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashen Sin da Amurka suna karfafa hadin gwiwa tsakaninsu a fannonin tattalin arziki da cinikayya
2009-12-01 12:24:54 cri
Tun ran 15 zuwa ran 18 ga watan Nuwamba, a karo na farko ne shugaba Barack Obama na kasar Amurka ya kawo wa kasar Sin ziyara. Shi ne shugaban kasar Amurka na farko da ya kawo wa kasar Sin ziyara bayan da ya hau kan mukamin shugabancin kasar Amurka cikin shekara daya. A cikin dimbin muhimman batutuwan da ke jawo hankulan kasashen Sin da Amurka, ko shakka babu, batun raya huldar tattalin arziki da cinikayya a tsakaninsu ya fi muhammanci. A lokacin da ake tinkarar rikicin hada-hadar kudi na duniya, kasa mafi ci gaba da kasa mai tasowa mafi girma a duniya suna bukatar neman hanyoyin karfafa yin hadin gwiwa a tsakaninsu a fannin tattalin arziki da cinikayya domin tinkarar rikicin cikin hadin gwiwa.

A cikin shekaru 30 da suka gabata, yawan kudin cinikayya da aka yi a tsakanin kasashen Sin da Amurka ya karu da ninki 130, wato tun daga dalar Amurka biliyan 2.5 a shekarar 1979 zuwa dalar Amurka biliyan 330 ko fiye a shekara ta 2008. A ran 16 ga wata, lokacin da yake zantawa da matasan kasar Sin a birnin Shanghai, Mr. Barack Obama na Amurka ya ce, huldar tattalin arziki da cinikayya tana karfafa huldar da ke kasancewa a tsakanin kasashen Sin da Amurka. Mr. Obama ya ce, "Cinikayya tana kawo tasiri ga zaman rayuwar jama'a a fannoni daban daban. Alal misali, na'urorin kwamfuta da tufafi da ake amfani da su a kasar Amurka kayayyaki ne da aka shigar da su daga kasar Sin. Kuma muna fitar da injuna iri iri zuwa kasar Sin. Irin wannan cinikayya tana samar da dimbin guraban aikin yi ga kasashen biyu da suke bakin tekun Pacific, jama'armu ma suna jin dadin zaman rayuwarsu mai inganci. A lokacin da ake raya cinikayya cikin daidaito, kasashen Amurka da Sin za su iya kara samun bunkasuwa a karin fannoni daband daban. Yanzu, kasashen biyu suna kokarin yin hadin gwiwar cikin hali mai yakini da ya dace. Sakamakon haka, kasashen biyu suna iya samun hanyar kafa huldar abokantaka a tsakaninsu kan muhimman batutuwan da duk duniya ke fuskanta tare. Wadannan muhimman batutuwa su ne batutuwan farfado da tattalin arziki da neman makamashi mai tsabta da rigakafin yaduwar makaman nukiliya da kuma batun tinkarar sauyin yanayin duniya tare da batun tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankunan Asiya, har ma da duk duniya."

Amma a waje daya, a gaban rikicin hada-hadar kudi na duniya, kasar Sin, wato wata babbar kasar da ke raya sana'o'in kere-kere da kasar Amurka wadda take kan gaba wajen sayayyen kayayyaki ba su iya tsira daga wannan rikici ba. A cikin farkon watanni 9 da suka gabata, yawan kudin cinikayya da aka yi a tsakanin kasashen Sin da Amurka ya kai dalar Amurka biliyan 211.8, wato ya ragu da fiye da kashi 10 cikin dari bisa na makamancin lokaci na bara. Daga cikinsu, yawan kudin kayayyakin da aka fitar da su daga kasar Sin zuwa kasar Amurka ya kai dalar Amurka biliyan 157.3, wato ya ragu da kashi 17 cikin dari. Sannan yawan kudin kayayyakin da aka shigo da su daga kasar Amurka zuwa nan kasar Sin ya kai dalar Amurka biliyan 54.5, wato ya ragu da kashi 12 cikin kashi dari.

A waje daya, kiki-kakar da aka yi a tsakanin kasar Sin da kasar Amurka a fannin cinikayya ya kara tsananta. A cikin shekarar da ake ciki, kasar Amurka ta haifar da matsaloli ta hanyar binciken kayayyaki kirar kasar Sin har sau 13. Wadannan matsaloli suna shafar naman tsuntsaye da tayoyi da takardu da bututun hakar mai da aka fitar da su zuwa kasar Amurka daga kasar Sin. Sakamakon haka, ita ma kasar Sin ta dauki matakan binciken kayayyakin Amurka, ciki har da kayayyakin da suke da nasaba da motoci da na kaji. Game da irin wannan halin da ake ciki a tsakanin kasashen Sin da Amurka, Mr. Yuan Peng, shugaban hukumar nazarin Amurka ta cibiyar nazarin huldar zamani da ke kasancewa tsakanin kasar Sin da kasashen waje ya ce, yawan kudin cinikayya da ake yi a tsakanin kasashen Sin da Amurka yana da yawa, sakamakon haka, an samu wasu matsalolin kiki-kaka, wadannan abubuwa ne da aka saba da ganinsu. Amma dole ne a gane cewa, wani muhimmin dalilin da ya sa a kan gamu da irin wadannan matsaloli shi ne har yanzu kasar Amurka ta ki amincewa da matsayin raya tattalin arziki irin na kasuwanci da kasar Sin ke dauka.

"Bisa kididdigar da bangaren Amurka ya yi, yawan kudin cinikayya da aka yi a tsakanin kasashen Sin da Amurka ya riga ya kai dalar Amurka biliyan 400, wannan wani babban adadi ne kwarai. Bai kamata a yi mamaki ba idan aka gamu da kiki-kaka da sabane-sabane bisa irin wannan halin da ake ciki. Amma, babban dalilin da ya sa aka samu matsaloli, kamar matsalar musamman ta kare tayoyi shi ne har yanzu kasar Amurka ta ki amincewa da matsayin raya tattalin arziki irin na kasuwanci da kasar Sin ke dauba. Kasar Sin ta yi shekaru 30 tana aiwatar da manufofin yin gyare-gyare da bude kofa ga kasashen waje, yanzu kasar Sin tana tsayawa tsayin daka wajen tsaro da kuma sa kaimi ga kokarin bin tsarin yin cinikayya cikin 'yanci. A wannan halin da ake ciki, idan har yanzu ba a amince da matsayinta na raya tattalin arziki irin na kasuwanci ba, ba daidai ba ne. A bangare daya, kasar Amurka tana kulawa da farashin musayar kudin Sin bisa ka'idojin tattalin arziki irin na kasuwanci da kasar Sin take bi, amma a bangare daban, kasar Amurka tana bincike da kuma ci wa kasar Sin tara kan kayayyakin da kasar Sin ke fitarwa zuwa kasar Amurka bisa matsayinta na raya tattalin arziki bisa shiri. Sabo da haka, matsala mafi tsanani da ke kasancewa a tsakaninsu ita ce, yaushe kasar Amurka za ta iya amincewa da matsayin raya tattalin arziki bisa ka'idojin kasuwanci da kasar Sin take bi? Idan ba ta iya daidaita wannan batu ba, shi ke nan, ba za a iya warware matsalolin cinikayya da ke kasancewa a tsakaninsu ba."

Abin da ya kamata a kula da shi lokacin da Barack Obama ke yin ziyara a kasar Sin shi ne, shugabannin kasashen Sin da Amurka dukkansu sun amince da cewa, za su yi fama da kowane irin tunanin kariyar cinikayya. A gun taron manema labaru da aka shirya, shugaba Hu Jintao na kasar Sin ya jaddada cewa, "Mun yi musayar ra'ayoyi kan halin da ake ciki a fannonin tattalin arzikin kasa da kasa da sha'anin kudi. Muna ganin cewa, yanzu tattalin arzikin duniya yana samun farfadowa, amma tushensu ba shi da karfi. Sabo da haka, bangarorin biyu sun jaddada cewa za su ci gaba da yin shawarwari da hadin gwiwa kan manufofin da ke shafar tattalin arziki daga dukkan fannoni. Kuma za su dinga yin shawarwari domin kawar da kiki-kaka da ke kasancewa a tsakaninsu a fannin cinikayya kamar yadda ya kamata."

Batu daban da ya fi jawo hankalin jama'a shi ne batun farashin musayar kudin Renminbi na kasar Sin. Game da wannan batu, Mr. Yao Jian, kakakin ma'aikatar kasuwanci ta kasar Sin ya ce, "Bisa kididdigar da bangaren kasar Sin ya yi, tun daga watan Janairu zuwa watan Oktoba na shekarar da muke ciki, yawan ribar da kasar Sin ta samu a fannin cinikayyar da ake yi a tsakaninta da kasar Amurka ya ragu da kashi 18 cikin dari. A waje daya, bisa kididdigar da bangaren kasar Amurka ya yi, yawan gibin kudin da kasar Amurka ta samu a wannan fanni ya ragu da kashi 15 cikin kashi dari. Sabo da haka, an gano cewa, yawan ribar da kasar Sin ke samu a wannan fanni yana raguwa. Cinikayyar da ake yi a tsakanin kasashen Sin da Amurka tana samun daidaito."

Game da wannan ziyarar da shugaba Barack Obama na kasar Amurka ya kawo wa kasar Sin, Mr. Yuan Peng, shugaban hukumar nazarin kasar Amurka ta cibiyar kasar Sin ta nazarin huldar zamani da ke tsakanin kasa da kasa ya ce, "A kan batun farashin musayar kudin Renminbi na kasar Sin, na amince da cewa, shugabannin kasashen biyu za su iya kara fahimtar juna sakamakon shawarwarin da suka yi, kuma za su iya samun wata hanya mai kyau domin daidaita batun raya cinikayya a tsakanin kasashen biyu cikin daidaito." (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China