in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin za ta yi namijin kokarin rage fitar da abubuwan da ke dumama yanayin duniya
2009-11-28 16:48:38 cri
A ran 27 ga wata, jakada Yu Qingtai, wato wakilin musamman na kasar Sin mai kula da shawarwarin da ake yi kan batun sauye-sauyen yanayin duniya ya bayyana cewa, kasar Sin za ta yi namijin kokarinta wajen rage fitar da abubuwan da ke dumama yanayin duniya bisa ka'idojin neman ci gaba mai dorewa. Yana fatan bangarori daban daban su sa rai ga sakamakon da kasar Sin za ta samu kamar yadda ya kamata, kuma su ba da sharhi kan matakan da kasar Sin za ta dauka cikin adalci bisa hakikanin halin da ake ciki.

A gun wani taron manema labaru da aka shirya a ran 27 ga wata, Mr. Yu Qingtai ya bayyana wa manema labaru manufofi da matakan da kasar Sin ta bayar, kuma za ta dauka wajen rage fitar da abubuwa masu dumama yanayin duniya.

Bisa sanarwar da gwamnatin kasar Sin ta bayar, an ce, ya zuwa shekara ta 2020, yawan abubuwa masu dumama yanayin duniya da za ta fitar zai ragu da kashi 40 cikin kashi dari zuwa kashi 45 cikin kashi dari bisa na shekara ta 2005. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China