A jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kanta, inda musulmai sun fi yawa a kasar Sin, musulmai sun sanya kyawawan tufafi, kuma sun shiga masallatan da ke wurare daban daban na jihar sun yi sallah domin neman fatan alheri. Bisa wani labarin da aka bayar, an ce, motocin taksi kusan dari 3 na birnin Urumchi, babban birnin jihar Xinjiang, sun yi sufurin fasinjoji ba tare da karbar kudi ba a wannan ranar murnar babbar sallah.
A jihar Ningxia ta kabilar Hui mai cin gashin kanta, inda musulmai fiye da miliyan 2 suke zaune, musulmai sun yi sallah kuma sun yanka tumaki domin murnar wannan babbar sallah.
Haka kuma a babban masallacin dake titin Niujie, wato masallaci mafi girma a nan birnin Beijing, musulmai fiye da dubu 6 wadanda suka zo daga kasashe daban daban sun yi sallah domin murnar wannan babbar sallah. (Sanusi Chen)