A yayin taron, ana ganin cewa, a gaban barazanar da rikicin hada-hadar kudi na duniya da ba safai a gan shi ba a tarihi ya yi da bala'u daga indallahi da su kan faru a kasar Sin, gwamnatin kasar ta tsaya tsayin daka kan matsayin daukar manufofin kasafin kudi cikin hali mai yakini da manufofin kudi da suka dace bisa hakikanin halin da ake ciki, har ma ta aiwatar da kuma kyautata jerin shirye-shiryen tinkarar rikicin hada-hadar kudi na duniya. Sabili da haka, tattalin arzikin kasar Sin ya soma samun farfadowa, har ma ya samu ci gaba.
Haka kuma a yayin taron, an nuna cewa, kasar Sin za ta tabbatar da manufofin raya tattalin arziki daga dukkan fannoni da ake aiwatarwa cikin hali mai dorewa. Bugu da kari, za ta kara mai da hankali wajen canja hanyoyin ci gaban tattalin arziki da tsarinsa, kuma za ta yi kokarin tsimin makamashi da rage fitar da gurbataccen abubuwan da suke gurbata muhalli, musamman za ta sa kaimi ga kokarin kara bukatu a kasuwannin cikin gida. (Sanusi Chen)