Mr. Jeremy Warner wanda ya rubuta wannan bayani kuma ya shahara sosai a kasar Ingila wajen ba da sharhi kan harkokin tattalin arziki. A cikin bayaninsa, bayan ya yi amfani da hotuna domin yin nazarin yadda kasashen Sin da Amurka suke fitar da kayayyakinsu, Mr. Jeremy ya nuna cewa, sakamakon manufar musayar kudi da kasar Sin ke aiwatarwa, yawan kayayyakin da kasar Sin ke fitarwa ya samu farfadowa, har ma ta fi samun karfi wajen shigar da kayayyaki daga kasashen waje.
Haka kuma, a kwanan baya, Mr. Shaun Rein, babban diraktan kamfanin nazarin kasuwanin kasar Sin ya bayar da wani bayani a kan shafin yanar gizo ta Forbes na kasar Amurka, inda ya ce, ra'ayin neman kasar Sin ta hau farashin kudin Renminbi da Mr. Paul Krugman wanda ya samu lambar yabo ta tattalin arziki ta Nobel ya dauka kuskure ne. A ganin Rein, ba ma kawai wannan ra'ayin Krugman zai lalata tattalin arzikin kasar Sin ba, har ma zai lalata moriyar masu sayayye na kasar Amurka da kokarin farfadowar tattalin arzikin duk duniya. (Sanusi Chen)