in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Labaru daga jaridun Afirka
2009-11-20 20:23:00 cri

A cikin shirinmu na yau, bari mu duba wani bayani da muka samu daga jaridar 'Daily Champion' ta kasar Nijeria, wadda aka buga a ran 19 ga wata, inda aka mai da hankali sosai kan sauyawar yanayin duniya.

Wasu kasashe masu tasowa sun shirya wani taron koli kan sauyawar yanayin duniya a kasar Maldives, inda suke son samun ra'ayi daya a babban taron Copenhagen da za a shirya a watan gobe, shugabannin da wakilai sun tattauna kan raya tattalin arziki ba tare da fitar da gawayi da ke dumamar yanayin duniya.

Shugaban kasar Maldives, mai masaukin baki na wannan taron koli mista Mohamed Nasheed ya yi kira ga dukkan kasashen da ke shan wahala sakamakon gawayi da kasashe masu tasowa da su hada kansu domin samun wata kyakkyawar makoma ta rage gawayi.

Nasheed ya yi jawabin cewa, ya ji bakin ciki sabo da ba a samu ci gaba a gun shawarwarin da aka yi kan sauyawar yanayin duniya. Sabo da haka, ya yi kira ga kasashe da suke fama da talauci da kasashe da suka fi shan wahala da gawayi da su gwada sha'awarsu ta amfani da makamashi irin na bola jari.

Jama'ar da suka halarci taron koli sun hada da wakilai da suka zo daga kasashen Sin, da Ghana, da Kenya, da Tanzania, da Bangladesh, da Nepal, da Vietnam, da France, da Japan, da Denmark, da Netherland, da Norway, da Rasha, da UK, da Amurka da dai sauransu.

Nasheed ya bayyana cewa, wannan taron koli ya sa kaimi ga kasashen da suke shan wahala da gawayi domin su samu matsayi daya kan shawarwari da za a yi a Copenhagen, da kuma kawo karshen wahalan.

A ganinsa, kasashen da suke da hangen nesa suna son raya tattalin arzikin tsimin makamashi, wadannan kasashe za su iya samun nasarori a nan gaba. Ya yi kira ga kasashe masu tasowa da su canza hanyar da suke bi wajen raya tattalin arziki yayin fitar gawayi, kuma su yi amfani da fasahohin tsimin makamashi.

Nasheed ya ce, wasu kasashe da ke shan wahala daga gawayi, da kuma wadanda ke da niyyar rage fitar da gawayi za su iya gabatar da bukatunsu ga kasashen yamma da babbar murya. Ya ce,

'Ba mu son mu daddale yarjejeniyar kisan kai, amm muna son yarjejeniyar kiyaye rayukanmu.'

Ministan muhalli na kasar Maldives Mohamed Aslam ya ce,

'Mun shafe shekaru goma muna jira, amma babu wani abin da ya canza, mun ki yarda da zama kawai ba tare da yin kome ba.'

Wani kwararre a fannin muhalli Mark Lynas, wanda ya taimaka wajen tsara shirin rage samar da gawayi a shekaru 10 masu zuwa na kasar Maldives, ya gaya wa mahalartan taron koli cewa, kasashen duniya sun bukaci kawar da gawayi, sa'an nan kuma za su iya 'yantar da duniya daga mawuyacin hali sakamakon sauyawar yanayi.

A watan Maris na shekarar da muke ciki, kasar Maldives ta sanar da cewa, ta yi shirin zama kasa ta farko wajen kawar da gawayi. Bisa abubuwan da aka tanada a cikin shirin Maldives, an ce, za ta canza hanyar da take bi wajen raya tattalin arziki, wato ba za ta yi amfani da mai ba, za ta yi amfani da makamashi irin na bola jari a yayin da take gudanar da dukkan ayyukan bunkasa tattalin arziki.

A farkon watan nan, shugaban kasar Maldives Nasheed ya sanar da wani shirin kafa wata tashar samar da wutar lantarki mai karfin iska a arewacin birnin Male, babban birnin kasar, wadda za ta iya samar da wutar lantarki da yawansu zai kai kashi 40 cikin dari da duk kasar take bukata, ta yadda za a iya rage gawayi da ake fitarwa da yawansa ya kai kashi 25 cikin dari.

Nasheed ya gaya mana cewa, ya kamata kasashe masu tasowa su cimma burinsu a taron Copenhagen, sabo da taron zai iya yanke shawara kan makomarsu.(Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China